Wa’azi, Waraka Ko Ceto, Shiriya Da Rahama
Wa’azi, Waraka Ko Ceto, Shiriya Da Rahama
A nan zan kawo abin da Sayyid Tabataba’i (qs) ya ambata a cikin tafsirinsa a karkashin wannan ayar a takaice[1]:
Ragib a cikin Mufradat ya ce: Al-wa’az: Ai kare wani da kiyaye shi daga aikata wani aiki tare da tsoratarwa. Khalil kuma ya ce: Shi tunatarwa ce domin a aikata wani aiki na alheri, ta hanyar yin bayanin da yake farkar da zuciya, samar da waraka ga kiraza, wanda hakan kuma kinaya ce da ke tafiyar da dukkan wasu siffofi marasa kyau masu jawo wa mutum tabewa da raunana masa rayuwarsa ta farin ciki da haramta masa alkairan duniya da lahira. Kuma an ambaci kiraza ne kawai saboda cewa su mutane zuciyarsu tana can kasan kirji ne, kuma sai aka lura cewa dan adam yana fahimtar duk abubuwan da yake sani ta hanyar zuciyarsa, kuma ta nan ne yake fuskantar lamurra, so ko ki, sha’awa da tsana, kwadayi, fata da buri, to sai suka kirga kirji a matsayin wajen adana abin da ke cikin zuciya na sirrori da siffofi na ruhi wadanda suke boye a cikin mutum na kyawawan dabi’u da munana.
Na ce: Hadisai sun nuna cewa lallai Qur'ani waraka ne hatta ga cututtuka da ke jikin mutane, kai an ma samu a wasu daga cikin hadisan da ke cewa da za a karanta surar Fatiha sau saba’in ga mamaci to zai tashi ya rayu, kuma hakan ba abin mamaki ba ne.
Ita kuma rahama; wata tasirantuwa ce a zuciya kebantacciya ta musamman ta yadda da zarar zuciyarsa ta lura da wata lalura ko gazawa daga waninsa zai shiga cikin damuwa har sai ya ga ya kawo masa dauki domin ganin an magance masa wannan matsalar tasa. Amma idan aka jingina ta ga Allah Subhanahu to za ta dauki ma’anar natija ce ba asalin tasirantuwa din ba, domin shi Allah ya tsarkaka daga tasirantuwa ga waninsa don haka sai waccan ma’anar ta yi daidai da kyautar Ubangiji marar iyaka da kuma falalarsa ga halittarsa da ya samar da su.
Na ce: Wannan daya ne daga hanyoyin sharhin wadannnan sifofin masu albarka wadanda fahimtar dangantakarsu ga Allah Tabaraka wa Ta'ala kamar yadda ake danganta su ga ababen halitta take da wuyar gaske.
Kuma idan ka kalli wadannan sifofin guda hudu wadanda Allah Ta'ala ya danganta su ga Qur'ani a cikin wannan ayar – ina nufin wa’azi, waraka ga abin da ke cikin kiraza, shiriya da rahama – sai ka kiyasta sashensu a kan sashe sannan sai ka komo zuwa ga shi Qur'ani za ka ga ayar tana bayani ne cikakke mai gamewa a kan dukkan tasirinsa a wajen kyau da kyautatawa tare da aikinsa tsarkakakke wanda yake ratsa rayuka da zukatan muminai tun a farkon lokacin da ya fara kwankwasar ji da saurarensu har daga karshe ya samu wanzuwa a cikin zukatansu.
Domin shi Qur'ani tun a farko zai fahimtar da su irin yanayin halin da suke ciki na gafala da ta lullube su kuma hayaniyar ‘yanci ta mamaye su, sai suka nutse cikin duhun rafkanuwa da kokwanto kuma sai zukatansu suka kamu da rashin lafiyar munanan dabi’u da dukkan munanan halaye abin kyama, to sai ya yi masu wa’azi[2] wa’azi kyakkyawa wanda zai fadakar da su game da bacci mai nauyi na gafala da suke ciki, ya kuma hane su daga mugayen abubuwan da suke boyewa da munanan ayyuka, sannan sai ya tunkuda su zuwa ga abubuwa na alheri da dacewa.
Sannan zai tsarkake masu munanan ayyukansu, kuma zai ci gaba da gusar masu da abubuwa masu cutar da hankula da cututtukan zukata daya bayan daya har sai ya isa ga na karshensu.
Sannan sai ya shiryar da su zuwa ga sani da ma’arifa ta hakika, kyawawan halaye masu karamci da ayyuka na gari, da shiriyar da za ta daga darajarsu kan daraja, ya dinga kusantar da su daga wannan matakin zuwa wancan har su isa zuwa ga matabbatar makusanta, sannan su yi nasara irin nasarar masu ikilasi.
Kuma zai lullube su da tufafin rahama, ya shigar da su gidan karamci, ya dora su a kan karagar ni’ima har daga karshe ya sada su da Annabawa, siddikai, shuhada da salihai, kuma wadannan sun kyautatu ga kasantuwa abokan tafiya. Sannan zai shigar da su a cikin bayinsa makusanta a cikin Illiyyina.
Saboda haka Qur'ani mai wa’azi da warkarwa ne ga abubuwan da suke cikin kiraza, mai shiryarwa ne zuwa ga madaidaiciyar hanya, mai baiwar rahama ne da izinin Allah Ta'ala, kuma cewa shi yana wa’azi da abin da ke cikinsa, yana warkar da kiraza, yana shiryarwa, yana fadada rahama da kansa, ba wai da wani lamari daban ba, wannan wani dalili ne da yake sadar da tsakanina - da bayinsa, domin shi wa’azi ne, waraka ne ga abubuwan da ke cikin kiraza kuma shiriya ce da rahama ga muminai.
[1] Al-Mizan; mujalladi na 10, a cikin tafsirin ayoyi na 57-70 na surar Yunus, amma abin da ake magana a kansa yana cikin aya ta 57 cikin fadin Allah Ta'ala: “Ya ku mutane! Lallai wa’azi ya zo maku daga Ubangijinku, da waraka ga abin da yake a cikin kiraza da shiriya da rahama ga muminai”, Yunus: 57.
[2] Kuma kai da kanka za ka ga haka a cikin surorin Makka wadanda suka sauka tun a farko-farko irinsu surar Muddassir da Muzzammil domin su ma’abotan iiqa’at a fili, wadanda suka yi amfani dakalmomi masu karfi ta yadda tasirinsu yake kasancewa kamar irin tsawar uwar lantarki wacce take aiki domin farkar da gafalalle kamar yadda abubuwan da suka kunsa ya mayar da hankali ne a kan yin wa’azi da tunatarwa ga mutuwa da lahira a halayen ranar kiyama a makomar makaryata, da bayanin sunnar Allah Ta'ala a cikin al'umma da makamantansu na azaba.