Magana Mai Nauyi
Magana Mai Nauyi
Idan aka ce mai nauyi ta yadda magana ko lafazi za su iya daukar wannan ma’ana, wato shi ne nauyi a kan rai (sha’awace-sha’awacen rai) domin yana takure sha’awace-sha’awacenta ba ya sakar mata mara, sai dai ma zai tsaftace ta, ya karfafe ta sannan ya jagorance ta. Kuma mai nauyi ne a kan hankali saboda abin da ya kunsa na sirrori wadanda jure su a wajen hankalin jabberai abu ne mai tsauri. Kuma mai nauyi ne a kan ruhi na abin da ke tattare da shi na takalifofi masu gajiyarwa da tarbiyantarwa, mai nauyi ne wanda a kansa ne ma Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi ishara da cewa: “Suratul Hud da Waqi’a sun tsofar da ni domin a cikinsu akwai (Fastakim) wato sai ka daidaitu kamar yadda aka umarce ka, kuma shi Manzon Allah (s.a.w.a) ya san nauyin wannan lamari.
Kuma asalin nauyin nasa saboda ya gangaro ne daga Allah mai girma, shi ya sa littafin sira (tarihi) suke nakalto yanayin da Annabi (s.a.w.a) yake shiga a yayin saukar wahayi gare shi. Qur'ani ma ya siffanta nauyin a cikin fadinsa: “Da mun saukar da wannan Qur'anin a kan dutse, da lallai ka ga dutsen yana mai tawali’u, mai tsattsagewa saboda tsoron Allah, kuma wadancan misalai muna bayyana su ne ga mutane, da fatan za su yi tunani” Hashri: 21.
Shi mai nauyi ne game da wanda ya yi riko da shi yake fuskanta, mai kokari wajen ganin ya tsayar da dokokinsa a cikin al'umma na daga wahalhalu da bala’oi. Allah Ta'ala ya ce: “Alif, Lam, Mim, Sad. Littafi ne aka saukar zuwa gare ka, saboda haka kada wani kunci ya kasance a cikin kirjinka daga gare shi, domin ka yi gargadi da shi, kuma tunatarwa ce ga muminai” A’araf: 1-2. Shi ya sa aka umarci Manzon Allah (s.a.w.a) da tsayuwar dare (sallar dare) da kuma damfaruwa da Allah Tabaraka wa Ta'ala da zurfafawa cikin neman kusanci domin hakan ya zama sila da dalili na samun jajircewa ta karbar sakon wato maganar nan mai nauyi, da jagoraci mai girma, kuma Allah Ta'ala ya yi masa alkawarin shi ne zai ba shi nasara, Allah Ta'ala ya ce: “Kuma da daddare sai ka yi tahajjudi da shi a kan kari gare ka (nafila), akwai tsammanin Ubangijinka ya tayar da kai a wani matsayi abin godewa” Isra’i: 79.