Madaidaici (Kayyim)

| |times read : 384
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Madaidaici (Kayyim)

Daga daidaitattun dabi’u, domin shi wannan Littafi mai tsayuwa ne tsayin daka wajen jagorantar bayi tare da nuna masu hanyar da za ta gyara masu rayuwarsu da tanadar masu dukkan abin da zai kai su ga samun sa’ada da dacewar duniya da lahira, kamar yadda yake tsayuwa kyam wajen gyaran zamantakewar iyali ko ta al'umma gabaki daya, kuma manhajin Qur'ani shi ne mafi daidaita a kan dukkan sauran manhajoji, shin manhajin nan na akida ne ko na shari’oi to dai shi ne ke kan gaba shi ke jagoranci a kansu, su kuma masu biyayya ne da kankan da kai da sallamawa hukuncin da ya tafi a kansa. Don haka hakikanin daidaito madaukaki a wannan rayuwar yana nan tare da Qur'ani. In dai mutane suna son su rayu cikin alkairi da sa’ada, ba kamar abin da suke aikatawa ba na nisantar manhajin Qur'anin suna jagorantar da hankulan ‘yan adam wadanda suka gaza, masu karkata a mafi yawancin lokuta zuwa ga son rai da maslahohi, kuma lallai hakika ayar Qur'ani ta riga ta yi shimfida na wannan daidaito din a yayin da ta siffanta shi da cewa babu karkata a gare shi, babu nakasa, babu barna da rauni haka nan ma babu gazawa a tattare da shi. Allah Ta'ala ya ce: “Kuma bai sanya karkata ba a gare shi” Kahfi: 1. Kuma daga cikin sharuddan daidaituwa da salladuwa a kan dan adam ga wanda yake son kai waninsa ga kamala, to da farko shi ya fara zama kammalalle din a kan kansa, domin wanda ya rasa abu, ba ya iya bayar da shi kamar yadda suke fada, daga cikin abin da yake lalura ba makawa ga mutum in yana son samun daidaito shi ne ya nema a gurin wanda babu nakasu, lahani, rauni ko gazawa a tattare da shi, wanda hakan bai taba tabbatuwa ga wani ba sai ga wannan Littafin mai girma da takwarorinsa siqlul asgar wato iyalan gidan Annabta (as), duk wani koma bayan wadannan to ba shi da hakkin jagorantar al'umma da daidaito da salladuwa a kansu. A cikin wannan ma’anar akwai hadisai masu yawa wadanda suke wajabta gabatar da Littafi da iyalan gidan Annabta a farko. “Kuma wanda ya bijire daga ambatona, to lallai ne rayuwa mai kunci ta tabbata gare shi” Da Ha: 124. Ai wato rayuwar takura da tsanani, kuma wannan sifa ce ta duk wanda ya bijirewa ambato da tuna Allah Tabaraka wa Ta'ala kuma zai kasance ya yanke wa kansa alaka tsakaninsa da mahaliccinsa Subhanahu, kuma zai kasance yana rayuwa nesa da Qur'ani mai girma, don kuwa zai kasance cikin takura, kaskanci, talauci da radadi saboda an zare rahamar Allah mai yalwa daga gare shi sai ya fadawa son rai, kwadayi da sha’awace-sha’awace wadanda ba su da iyaka, sai ya wayi gari cikin firgici na tsoron mutuwa, a saboda haka sai ya yi asarar duniyar wacce ita ce kololuwar hankoronsa kuma a lahira ba shi da wani rabo, sannan zai ta rayuwa cikin kokarin kiyaye abin da ke hannunsa gudun kada ya rasa shi, kuma tabbas zai rayu cikin gajiya da rauni domin zai yi ta lallage a fako yana mai tunanin yana hango ruwa ne daga nesa. Babu abin da zai iya samu wanda yake zaton akwai jin dadinsa a cikinsa, har daga karshe shi da kansa zai gane cewa lallai yana yaudarar kansa ne kawai, a saboda haka sai ya nemi canza wani abun daban, misali zai iya zaton cewa jin dadinsa yana cikin samun kudi don haka sai ya tara miliyoyi, amma sai ya gano jin dadin bai samu ba, to sai ya yi zatonsa a cikin manyan gidaje na alfarma, don haka sai ya gina gidaje na ban mamaki wadanda ido bai taba ganin irinsu ba, amma sai ya rasa jin dadin a nan din ma, sai ya yi zatonsa a cikin mata, don haka sai ya nemi mata masu tarin yawa ya yi ta sheke ayarsa da su, amma sai ya samu kansa tura ta kai masa har bango. To sai abin da Allah ya fada a Littafinsa mai tsarki ya misaltu a kansa (ya zama misdakin wannan ayar): “Sannan a lokacin da ya ga wata yana mai bayyana; sai ya ce: Wannan ne Ubangijina”. Wata a nan kinaya ce ta dukiya to sai ya yi zaton su ne Ubangijinsa masu samar masa da jin dadi, “Sannan a lokacin da ya fadi”. Ya zama bai samu biyan bukatarsa a nan ba; “Sai ya ce: Ni ba ni son masu faduwa”. “Sannan a lokacin da ya ga rana tana bayyana, sai ya ce: Wannan ita ce Ubangijina” Wannan kuma kinaya ce mai ishara kan wasu al’amuran na duniya, “Sai ya ce: Wannan shi ne Ubangijina, shi ne mafi girma” kuma wannan shi ne zai samar min da sa’ada da natsuwar zuciya domin wannan shi “Shi ne mafi girma”.    

            Amma mafi girman tasirin shi ne wato: “Sannan a lokacin da ya fadi”, ya ga wannan sabon Ubangijin shi ma ya gaza wajen samar masa da sa’ada da jin dadi, sai ya ce: “Ni ba ni son masu faduwa”, to kuma wadannan iyayen gijin raunana wadanda ba su iya mallakawa kawukansu wata cuta ko wani amfani ballanta su mallakawa wasunsu. A sannan idan dai shi muklisi ne a cikin bincikensa zuwa ga gaskiya to za a rubuta masa shiriya sai ya fadi abin da muminai suke fada ya ce: “Ya mutanena! Lallai ne ni mai barranta ne daga abin da kuke yi na shirka. Lallai ne ni na fuskantar da fuskata ga wanda ya kaga halittar sammai da kasa, ina mai karkata zuwa ga gaskiya, kuma ba ni cikin mushirikai” An’am: 76-79. Idan kuma bai kasance cikin masu shiryuwa ba, to za a rubuta tabewa a kansa, sai jawabinsa ya zama: “Kuma wadanda suka kafirta ayyukansu kwatankwacin kawalwalniya ga fako suke, ta yadda mai jin kishirwa yana zatonsa ruwa ne, har sai idan ya je masa bai iske shi komai ba, sai ya samu Allah a wurinsa, sai ya cika masa hisabinsa, kuma Allah mai gaggawar sakamako ne” Nur: 39.

Wannan kuma zai wanzu cikin tabewa, bata da takuruwa a tsakanin kusantowar mutawa wacce za ta iya daukarsa a kowane lokaci, da kuma zama cikin kwadayi da hadamar tara dimbin dukiya, Allah ya ce: “Kuma lallai ne zaka same su mafiya kwadayin mutane a kan rayuwa” Bakara: 96. Kuma za ka ga mafi yawancin dabi’un can na kunar bakin wake suna faruwa ne a kasashen da suke da raunin tattalin arziki wadanda suke rayuwa cikin cututtuka saboda yawan cin abinci ba kakkautawa, wanda kuma asasin wannan sharrin da suke rayuwa a cikinsa shi ne kasancewar ruhinsu ya zama fankam fayau.

        Allah ya ce: “Hakika wani haske da wani Littafi mai bayyanawa ya zo maku daga Allah. Da shi, Allah yana shiryar da wanda ya bi yardarsa zuwa ga hanyoyin aminci, kuma yana fitar da su daga duffai zuwa ga haske da izininsa, kuma yana shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya” Ma’ida: 15-16. Shi haske ne domin lallai yana haskaka zuciyar mumini, tun a farko sai ya tsarkaketa daga tsatsar sabo da dattin zunubbai, sannan sai ya tace farfajiyarta domin ta shirya karbar tajalli na gaskiya, kuma shi haske ne na al'umma da wuraren zamantakewarsu, yana shiryatar da su zuwa ga bin nizami wanda zai kai su ga samun dacewa.

Wani abin birgewa dangane da nau’in magana ta Qur'ani shi ne cewa sai ya sanya lafazin haske a matsayin tilo, duffai kuma jam’i, domin ita hanyar gaskiya kwara daya ce rak ba ta karkasuwa adadi-adadi, ko da hanyoyin isa gare ta da misdakokinta sun karkasu, Allah Ta'ala ya ce: “Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya” Fatiha: 6. Amma duffai suna da yawa kuma gumakan da suke toshe hanyar zuwa ga Allah Tabaraka wa Ta'ala su ma suna da tarin yawa.

Daga cikin tasirori da albarkokin Qur'ani cewa lallai shi yana shiryar da wanda ya bi yardar Allah zuwa ga hanyoyin aminci, kuma farkon amincin da za a yi masa ni’ima da shi, shi ne amincin natsuwar rai da sakankancewar zuciya da lafiyayyen tunani; “To ku saurara! Da ambaton Allah zukata suke samun natsuwa” Ra’ad: 28. Sannan sai aminci a cikin dangi da iyali wadanda suka taso cikin koyarwar musulunci da Qur'ani; “Kuma akwai daga ayoyinsa, ya halitta maku matan aure daga gare ku, domin ku natsu zuwa gare ta, kuma ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku, lallai a cikin wancan akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani” Rum: 21. Sannan kuma sai aminci tsakanin mutane a cikin unguwanni da garuruwa a lokacin da dabi’un musulunci suke jagorancinsu “Sai kuka wayi gari albarkacin ni’imarsa ‘yan uwan juna” Aali Imran: 103. “Muhammad Manzon Allah ne, kuma wadannan da ke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu” Fat’hi: 29. “Kuma suna fifita wadansu a kan kawukansu, koda suna da wata lalura” Hashri: 9.