Mai Girma (Majid)

| |times read : 469
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Mai Girma (Majid)

Malam Ragib a cikin littafinsa Mufradat ya ce: Almajdu: Yalwatawa a cikin karamci, jalala ko daukaka, kuma asalinsa yana nan a cikin fadinsu (rakuma sun daukaka) idan rakuman suka samu kansu a yalwatacciyar makiyaya mai fadi, to sai aka saiffanta Qur'ani da wannan ma’anar ta majid saboda yawan abubuwan da ya kunsa da karamomin duniya da na lahira, kuma a kan haka ne aka siffanta shi da karim, wato mai karamci a cikin fadin Allah Ta’ala: “Lallai ne shi (wannan Littafin), hakika abin karantawa ne mai daraja da karamci” Waqi’a: 77. Saboda yalwatar kyautarsa da yawaitar badawarsa, kuma a cikin sharhin sifar (Mubarak) mun yi ishara game da wadannan alamomin nasa masu fadi.