Buwaya

| |times read : 373
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Buwaya

Wannan sifar tana nufin cewa samuwarsa ba abu ne sasauka ba, domin lallai shi yana cikin wani Littafi (Lauhul Mahfuz) tsararre kuma madaukakan hakikokinsa suna nan a taskace a cikinsa, amma wadannan kalmomin ba komai ba ne sai misalai domin kusanto da ma’anoni a kwakwalwar dan adam wacce take samun natsuwa da madda kuma wacce ba ta yunkurawa domin takai ga gacin gane wadancan hakikokin, na’am sai dai akwai wadanda suke iya isa da kaiwa gare ta su kuma wadannan su ne wadannan da aka tsarkake su aka tafiyar da dukkan kazanta daga gare su kuma aka tsarkake su tsarkakewa, kuma su ne alayen Muhammad (s.a.w.a), kuma lallai a wani kauli na Amirul Muminina (as) yana cewa: Tabbas hakika mu, ba mu mallaki wani ilimi sama da fahimtar wannan Littafin ba, kuma shi Littafin mabuwayi ne, wato yana kore samuwar makamancinsa, kuma lallai haka din yake, domin cewa shi zance ne na wanda wani abu bai zama kamar tamkarsa ba, kuma mabuwayi ne wato kutsowar wani mummuna cikinsa ba mai yiwuwa ba ne, don haka sai ya kasance daidai da ma’anar ayar nan madaukakiya mai cewa: “Lallai mu ne muka saukar da ambato (wato Qur'ani), kuma lallai mu hakika masu kiyayewa ne gare shi” Hijr: 9. Kuma shi mabuwayi ne da ma’anar cewa shi mai tankwasawa ne, mai yin galaba kuma mai rinjaye domin cewa shi kalmar Allah ce, kuma kalmar Allah ita ce madaukakiya, don haka shi madaukaki ne a kan komai kuma ba a daukakuwa a kansa, sannan matsayarsa ko yaushe ita ce salladuwa da shugabantar bayi da tasarrufi a cikin sha’anoninsu, kuma shi mabuwayi ne da ma’anar cewa shi abin nema ne kamar yadda aka ce wai dukkan samamme mai gundura ne, kuma dukkan wanda ya bace abin nema ne, to kuma shi wannan Littafin abin nema ne ga duk wanda yake neman ya samu iso a gurin Allah Tabaraka wa Ta'ala.