Mubarak

| |times read : 407
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Mubarak

Sifa ce ga Qur'ani wacce take nufin mai yawan albarka, kuma haka abin yake ta bangarorinsa daban-daban domin shi mai albarka ne tun daga mahallin saukarsa, kasantuwar ya sauka ne daga gurin Allah Ta'ala, mai falala da ni’imar da ba ta da iyaka da adadi, mai albarka a mahallin da ya sauka wacce ita ce zuciyar Manzon Allah (s.a.w.a), kuma mai rahama mai karamcin da aka aiko shi rahama ga talikai. Kuma mai tasirin da ke da tarin albarka don a cikinsa akwai shiriya, alheri, sa’ada ta duniya da lahira, kuma a cikinsa akwai tsarin rayuwar ‘yan adamtaka, daidaitonta da kiyaye muruwarta da al’ummarta, kuma a cikinsa akwai aminci da natsuwa, kuma mai tarin albarka ne a cikin hajaminsa (girmansa), shi Littafi ne kwara daya rak, sai dai duk wasu mabubbugar wasu ilimummuka da ma’arifa suna kamfata ne daga gare shi, kuma shi idon ruwa ne mai gudana wanda ba ya kafewa, a saboda haka ne za ka samu masana usul, fikihu, nahawu da adabi da mufakkirai, masana ilimin siyasa, ilimin zamantakewar al'umma, tattalin arziki, likitanci, masu shari’a da shugabanni suna dauka daga gare shi, suna kafa hujja da ayoyinsa, kuma a haka zai ci gaba da wanzuwa har abada yana bayarwa, wanda wannan kawai ya isa dalilin da zai tabbatar da cewa ya sauka ne daga gurin Allah, domin wadannan ilimummukan gaba ki dayansu ba za a same su a cikin da yawan littafai ba wadanda za su iya dunkule ilimomin irin haka ba. Shi mai yawan albarka ne da yawan da ya kai matsayin da wasu da yawa sun shiriya ta hannunsa kuma zukatansu da hankulansu sun yi annuri a albarkacinsa.