Sharhi Na Wasu Daga Cikin Sifofin Qur'ani
Sharhi Na Wasu Daga Cikin Sifofin Qur'ani
Sai dai wannan dunkulallen sharhin ga sifofin Qur'ani ba zai wadatar ba, a saboda haka ne nake ganin akwai bukatar gabatar da sharhi mafi yalwa ga wasu daga cikin wadannan sifofin wadanda suke da tasiri a cikin rayuwa ta zamantakewar al’ummu da kyawawan dabi’u, tare da barin sauran sifofin wadanda ba wadannan ba zuwa ga littafan tafsirai masu bayani mai tsawo game da sauran ayoyin da na ambata a cikin jawabina. Koda yake dai zan ambaci wadannan sifofin ba wai don a samu masaniya ko ilimi a kan Qur'ani kawai ba, a’a sai dai don a samu masaniya da ilimi a kan Ahlul Baiti (as) domin cewa su takwarorin Qur'anin ne, kuma su iri guda ne da ba su rabuwa da juna, to idan Qur'ani yana furuci da gaskiya to su ma suna tare da gaskiya din ne kuma gaskiyar tana tare da su, kuma shi bata ba ta je masa, su kuma ma’asumai ne, idan Qur'ani madaidaici ne mai saidaruwa a kansu, to su ma (amincin Allah ya tabbata a gare su gabaki dayansu) suna da wannan daidaito da cancanta din kuma suna da saidara a kan mutane domin su ne Imamansu, shugabanninsu da jagororinsu kuma su ne mafiya cancanta gare su bisa ga kawukansu; da sauransu.