Qur'ani Yana Siffanta Kansa Da Kansa

| |times read : 492
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Qur'ani Yana Siffanta Kansa Da Kansa

         Sai dai mafi muhimmanci daga wannan shi ne in karanto maku wani sashe na ayoyi wadanda Qur'ani mai girma da kansa ya siffanta kansa da su domin mu kara saninsa, domin cewa na san wancan cewa shi magana ce ta mafi alherin masu yin magana. Ta hanyar wadannan ayoyin za ka san girma da jalalar wannan Littafin da daukakar alamominsa da albarkarsa:

1- “Wannan bayani ne ga mutane, kuma shiryuwa ce da wa’azi ga masu takawa” Aali Imran: 138.

2- “Lallai ne mu, mun saukar zuwa gare ka, Littafi da gaskia, domin ka yi hukunci a tsakanin mutane” Nisa’i: 105.

3- “Ya ku mutane! Hakika wani dalili daga Ubangijinku ya zo maku, kuma mun saukar da wani haske bayyananne zuwa gare ku. To amma wadanda suka yi imani da Allah kuma suka yi riko da shi, to zai shigar da su cikin wata rahama daga gare shi da wata falala, kuma ya shiryar da su zuwa gare shi ga tafarki madaidaici” Nisa’i: 174-175.

4- “Hakika wani haske da wani Littafi mai bayyanarwa ya zo maku daga Allah. Allah yana shiryarwa da shi duk wanda ya bi yardarsa zuwa ga hanyoyin aminci, kuma yana fitar da su daga duffai zuwa ga haske da izininsa. Kuma yana shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya” Ma’ida: 15-16.

5- “Kuma da lallai su, sun tsayar da Attaura da Linjila da abin da aka saukar zuwa gare su daga Ubangijinsu, hakika da sun ci daga samansu da kuma karkashin kafafunsu” Ma’ida: 66.

6- “Ka ce: Ya ku mutanen Littafi! Ba ku zama a kan komai ba, har sai in kun tsayar da Attaura da Linjila da abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku” Ma’ida: 68.

7- “Ba mu bar komai daga cikin Littafi ba (babu wani abu wanda ya yi saura da ba mu kawo ba a Littafi” An’am: 38.

8- “Kuma wannan Littafi ne, mun saukar da shi mai albarka ne” An’am 92.

9- “Kuma idan an karanta Qur'ani, sai ku saurara daga gare shi ku kuma yi shiru, domin a yi maku rahama” A’araf: 204.

10- “Ya ku mutane! Lallai wa’azi ya zo maku daga Ubangijinku, da waraka ga abin da yake a cikin kiraza da shiriya da rahama ga muminai” Yunus: 57.

11- “Lallai ne wannan Qur'ani yana shiryarwa ga halayen da suke mafi daidaita kuma yana bayar da bushara ga muminai wadanda suke aikata ayyuka na kwarai” Israi’i: 9.

12- “Allah ya sassaukar da mafi kyawon labari, Littafin da (ayoyinsa) mutashabihai (wato masu kama da juna) ne, wanda ake maimaita karatunsa, fatun wadanda suke tsoron Ubangijinsu suna karkarwa saboda shi, sannan fatunsu da zukatansu suna yin laushi saboda ambaton Allah, waccan ita ce shiryarwar Allah, yana shiryar da wanda yake so da ita, kuma wanda Allah ya batar, to ba shi da wani mai shiryarwa” Zumar: 23.

13- “Kuma lallai shi hakika littafi ne mabuwayi.  Barna ba ta je masa daga gaba gare shi, kuma ba ta je masa daga baya gare shi. Saukarwa ce daga mai hikima, abin gidiya” Fussilat: 41-42.

14- “Allah shi ne wanda ya saukar da Littafi da gaskiya da sikeli” Shura: 17.

15- “Kuma lallai ne shi a cikin uwar Littafi (Lauhu Mahfuz) a wurinmu, hakika madaukaki ne, mai hikima” Zukhruf: 4.

16- “Kuma wanda ya makanta daga barin hukuncin mai rahama, to za mu lullube shi da shaidan, wato shi a gare shi aboki ne makusanci” Zukhruf: 36.

17- “A saboda haka ka yi riko da ga abin da aka yi wahayi da shi zuwa gare ka. Lallai ne kai, kana a kan hanya madaidaiciya. Kuma lallai ne shi Ambato ne gare ka da ga jama’arka, kuma da sannu za a tambaye ku (game da shi)” Zukhruf: 43-44.

18- “Wannan (Qur'anin) ga mutane wani dalili ne na samun basira da shiriya da rahama, (amma) ga mutanen da suke da yakini” Jasiya: 20.

19- “Shin to, ba za su yi tadabburi a cikin Qur'ani ba, ko kuwa a kan zukatansu akwai kulli ne”? Muhammad: 24.

20- “Qaf, ina rantsuwa da Qur'ani mai girma (cewa kai Manzon Allah ne)” Qaf: 1.

21- “Kuma lallai ne hakika mun saukake Qur'ani domin tunawa, shin ko akwai mai tunawa”? Qamar: 40.

22- “Lallai ne shi (wannan Littafin), hakika abin karantawa ne mai daraja. A cikin wani Littafi (Lauhul Mahfuz) tsararre. Babu mai shafa shi, face wadanda aka tsarkake” Waqi’a: 77-79.

23- “Shin lokaci bai yi ba ga wadanda suka yi imani zukatansu su yi tawali’u ga ambaton Allah da abin da ya sauka na gaskiya ba? Kada su kasance kamar wadanda aka baiwa Littafi gabanin haka, sai zamani ya yi tsawo a kansu, saboda haka zukatansu suka kekashe, kuma da yawa daga cikinsu fasikai ne” Hadid: 16.

24- “Da mun saukar da wannan Qur'ani a kan dutse, da lallai kaga dutsen yana mai tawali’u, mai tsattsagewa saboda tsoron Allah, kuma wadancan misalan muna bayyana su ne ga mutane, da fatan za su yi tafakkuri” Hashr: 21.

25- “Kuma ka kyautata karanta Qur'ani daki daki. Lallai ne mu za mu jefa maka magana mai nauyi” Muzzammil: 4-5.

26- “Aaha! Shi Qur'ani ne mai girma. A cikin Lauhil Mahfuz (wanda aka taskace)” Buruj: 21-22.

27- “Lallai ne shi (Qur'ani), hakika magana ce mai rarrabe gaskiya daga karya. Kuma shi, ba rarraunan zance ba ne” Dariq: 13-14.

28- “Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya saukar da Littafi a kan bawansa kuma bai sanya karkata ba a gare shi. Madaidaici, domin ya yi gargadi da azaba mai tsanani daga gare shi, kuma ya yi bushara ga muminai wadanda suke aikata ayyuka na kwarai” Kahfi: 1-2.

29- “Kuma mun sassaukar da Littafi a kanka, domin yin bayani ga dukkan komai da shiriya da rahama da bushara ga masu mika wuya (musulmai)” Nahl: 89.

30- Kuma wanda duk ya bijire daga ambatona, to hakika rayuwa mai kunci ta tabbata gare shi, kuma za mu tayar da shi a ranar kiyama yana makaho” Da ha: 124.

           Wadanda wasu ne daga cikin siffofin da Qur'ani yake siffantuwa da su da kyawawan natijoji; domin shi Littafi ne mai albarka, mai girma, mai karamci kuma madaukaki. Shi bayani ne, kuma shiriya ce da wa’azi da rahama da waraka da ambato da haske ya sauka da gaskiya domin ya yi hukunci a tsakanin mutane, kuma ya saka muminai a cikin rahamar Allah da falalarsa ya kuma shiryar da su a kan hanya madaidaiciya, kuma shi madaukaki ne mai hikima, kuma shi wani dalili ne na samun basira ga mutane, kuma zance ne mai nauyi mai rarrabewa sannan kuma shi ba rarraunan zance ba ne, a saboda haka – ai wato hakikokinsa wadanda suka sanya lafuzzan nan nasa suka zama wani mazubi gare su, wadanda kamar wani misali ne domin kusanto da wadannan hakikokin da ma’anoni masu zurfi ga tunani – yake a cikin Littafi Maknun (tsararre) Lauhul Mahfuz babu mai shafarsa kuma babu wanda zai iya isa ga fahimtar hakikaninsa ciki da bai dinsa sai wadanda aka tsarkake daga barin zunubbai, sabo da laifuka, kuma madubin zuciyarsu ya tsarkaka daga dukkan datti, sai zuciyar ta wayi gari tana hango dukkan shafukan Lauhul Mahfuz kamar yadda suke. Amma wasunsu ba su da wannan iko da kudurar ta karbarsa sai dan abin da ba a rasa ba na kamala da suka samu; “Ya saukar da ruwa daga sama, sai koramu suka gudana daidai gwargwadon kowanensu” Ra’ad: 124.

An umarci mutane da su yi tadabburinsa, su karanta shi daki daki, su yi riko da shi, su saurara a yayin da ake karanta shi, kuma da ya kasance daga wurin wanin Allah, hakika da sun samu a cikinsa sabawa juna mai tarin yawa. To idan suka tsayar da shi, suka yi riko da shi, hakika za su ci daga saman kawukansu, da kuma daga karkashin kafafunsu, da sun tausasa da kaskantar da zukatansu, da sun zama masu cancanta da baiwoyin Ubangiji, amma idan suka bijire daga gare shi to za su wayi gari a cikin rayuwa mai kunci, za su fada cikin tarkon shaidanu har su wayi gari sun zama makusantansu, sai zukatansu su kekashe su zamanto kamar duwatsu, ko mafi tsananin kekashewa, kuma lallai ne daga duwatsu hakika akwai abin da maremari ke bubbuga daga gare shi, kuma lallai ne daga gare su hakika akwai abin da yake tsattsagewa har koramu suna fita daga gare su, kuma lallai ne hakika daga gare su akwai abin da yake fadowa domin tsoron Allah, kuma zukatan da suka yi nisa daga Qur'ani da ambaton Allah Subhanahu sun riga sun kurmance sun bushe babu ko digo na ruwan koramar ma’arifa da yake gudana a cikinsu; “Kuma wadancan misalai muna bayyana su ne ga mutane, da fatan za su yi tafakkuri” Hashr: 21.