Dalilan Da Suke Sa Wa A Girmama Qur'ani
Dalilan Da Suke Sa Wa A Girmama Qur'ani
Hakika bayanan da suka gabata suna bayyana irin muhimmancin da Qur'ani yake da shi a sarari, zan takaita su tare da fito da wasu sababbin nukudodin da ba mu ji su daga ayoyi masu girma da madaukakan hadisai ba:
1- Lallai Qur'ani babban magani ne mai warkar da dukkanin cututtuka, tun daga cututtukan zukata da rayukan ‘yan Adam, da na rayuwarsu ta zamantakewa kai har ma da na gabban jikinsu baki daya, kamar yadda zai zo nan gaba cikin madaukakan hadisai.
2- Rashin gimsuwa da shi da kuma neman isa ga kamala ta har abada a duniya da lahira – wanda hakan shi ne hadafi mafi daukaka kuma makura – da shiryuwa da shiriyarsa tare da riko da hanyarsa, kuma shi Qur'ani abu ne mai kara wa mutum daukaka da isa ga kamala, domin duk lokacin da amfanuwar mutum da shi ta karu to yana kara samun cikar kamala ne.
3- Lallai duk wanda ya girmama Qur'ani to ya yi koyi da Manzon Allah (s.a.w.a) da Ahlul Baitinsa masu girma (as), kamar yadda Allah Ta'ala ya umarce mu da mu yi: “Lallai abin koyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah, ga wanda ya kasance yana fatan samun rahamar Allah da ranar lahira, kuma ya ambaci Allah da yawa” Ahzab: 21.
4- Lallai Qur'ani sako ne na cikakken hakikanin masoyi, a al’adar mutum kuwa ba ya gajiyawa da karanta sakon hakikanin masoyinsa, da kwadayin duba ga sakon, da dogon nazari dangane da ma’anonin da sakon ya kunsa, shi kuwa Allah Ta'ala shi ne masoyi na hakika wanda babu kamarsa, domin shi so; ko dai ya kasance saboda kamala da kyautar wanda ake so din, to kuma dukkan siffofin kamala da kyawawan sunaye sun tattara ga Allah Ta'ala; ko kuma ya kasance saboda gangarowar wani alheri da kyauta daga gare shi, shi kuwa Allah shi ne mai ni’imtawa mai yin falala da kyautar da ba ta da iyaka har ga wanda bai cancanta ba kuma har ga bayinsa masu sabo; Allah yana cewa: “Kuma koda za ku nemi kidaya ni’imar Allah, ba za ku iya kididdige ta ba” Nahl: 18. Haka lamarin yake. Kuma a irin wannan ma’anar ne ya zo a ruwaya daga Imam Sadik (as) cewa ya ce: “Qur'ani alkawarin Allah ne ga bayinsa, don haka ya kamata ga bawa musulmi ya yi duba ga wannan alkawari ya kuma karanta daga gare shi aya hamsin a kowace rana”[1].
5- Akwai sakamako mai girma da lada mai tarin yawa wadanda ba su da iyaka da ake bai wa makarancin Qur'ani da mai yin tadabburi a cikin ayoyinsa, nan gaba za mu karanto hadisai da izinin Allah Ta'ala.
6- Shi Qur'ani kasantuwarsa Littafi ne mai ruhi, kuma mai wanzuwa har abada a kowane zamani da guri, a saboda haka abubuwan da ya magance a baya ba su takaita da wani zamani banda wani ba, a saboda haka ne ake da izinin amfana da Qur'ani domin magance sababbin abubuwa masu aukuwa, da sannu za mu bijiro da dama daga cikinsu a cikin bahasosin da za su zo a matsayin wata fikira wadda za mu kwatanta tsakanin zamanin jahiliyyar farko da jahiliyyar yanzu, kuma a game da wannan ma’anar akwai ruwaya daga Haris Al-A’awar inda ya ce: “Na shiga masallaci, sai na tarar da mutane suna ta maganganu na izgili ga hadisai, sai na wuce gurin Ali (as) na ce: Ba ka ga mutane suna ta izgili da hadisai a cikin masallaci ba? Sai ya ce: Tabbas sun aikata hakan? Sai na ce: Eh, sai ya ce: Ka sani cewa na ji Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: Fitina za ta auku, sai na ce: Mece ce mafita daga gare ta? Sai ya ce: Littafin Allah, a cikin Littafin Allah akwai labarin wadanda suka gabace ku, da labarin wadanda za su zo daga bayanku da hukuncin da ke a tsakaninku. Littafin Allah mai rarrabewa ne babu wasa a cikinsa, shi ne wanda idan wani ya barshi bisa jabberanci Allah zai karairaya shi, wanda kuma ya nemi shiriya daga waninsa Allah zai batar da shi, shi igiyar Allah ce mikakkiya kuma ambaton Allah ne mai hikima sannan shi hanya ce mikakkiya…”[2].
7- Koyon sanin ma’arifa, ilimoma da asrarai wadanda aka kunsa a cikinsa, ta yadda misali kamar Amirul Muminina (as) wanda Abdullah ibn Abbas hibrul Umma kuma daya daga cikin masu tafsirin Qur'ani yake siffanta iliminsa da cewa: Idan aka kwatanta ilimina da na dukkan sahabban Manzon Allah (s.a.w.a) da ilimin Ali (as) to kamar kwatankwacin digo ne a teku. Ina cewa misalin Ali (as) a iliminsa (An ce da shi: Shin akwai wani abu na daga ilimin wahayi a wajenku? Sai ya ce: A’a ina rantsuwa da wanda ya halicci komai da komai sai idan Allah ya bai wa bawa fahimta cikin Littafinsa”[3].
A cikin Littafin nan akwai akidodi na gaskiya, kyawawan halaye madaukaka, shari’oi masu cike da hikima, nukudodi masu gayar hikima da balaga da kyakkyawan zance wanda ya dace da dukkan bukatu, kuma a cikinsa akwai sirrorin halitta, abubuwan ban mamaki na halittu, da a can cikin jikin mutum, a sasanni da dabi’a, a cikinsa akwai abin da hankulan masu bincike bai iya ganowa ba. Wannan kuma ba yana nufin wannan Littafi ne na physics ko kimiyya ko falaki ko ilimin likitanci ta yadda har za a iya bijiro masa da kurakuransu da gazawarsu ba, a’a shi wani Littafi ne na shiriya da gyara yana dorawa kowane bangare wazifarsa domin ya cimma hadafinsa na shiryarwa. Kuma wadannan ilimimmukan gabaki dayansu suna afkuwa cikin wannan hadafin sai ya dauki abin da ya sauwaka na tabbatuwar hadafinsa.
8- Kubuta da tsira daga korafin da Qur'ani zai kai idan aka kaurace masa, kamar yadda ya zo a hadisin da ya gabata (abubuwa guda uku za su kai korafi….) kuma korafin da Qur'ani zai kai a wurin Allah Ta'ala, to ba a mayar masa da shi, kamar yadda ya zo a hadisi a yayin siffanta shi da cewa: “Mai jayayya ne da gaskiya” ai cewa shi jayayyarsa a kan gaskiya take, kuma shi za a baiwa gaskiyar, kuma abin da yake karfafa wannan da’awar shi ne ainahin korafin da Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi wanda Qur'ani ya ambata: “Ya Ubangijina! Lallai jama’ata sun riki wannan Qur’anin abin kauracewa” Furqan: 30.
9- Samun tsira ta hanyar ceton Qur'ani, kamar yadda hadisi ya siffanta shi da cewa: Shi Qur'ani a kan kansa shi ceto ne kuma mai yin ceto (wato waraka ne mai warkarwa), a cikin siffantawar da hadisi ya yi masa yana cewa: “Qur'ani zai kasance mai bayar da kariya ga makarancinsa – wato zai zama wani mai katangewa kuma mai gadin makarancinsa daga wahalhalu da tsanani – a ranar kiyama. Zai ce: Ya Ubangiji dukkan wani ma’aikaci an ba shi ladar aikinsa, banda wanda ya yi aiki da ni, to ina rokonka ka ba shi mafi girman karamcinka. Ya ce: Sai Allah mabuwayi da daukaka ya tufatar da shi wasu tufafi na musamman na aljanna sannan a dora masa wani kambu a kansa na karamci, sannan sai ya ce: Shin mun gamsar da kai game da lamarinsa? Sai Qur'ani ya ce: Ya Ubangiji lallai na yi fatan a yi masa fiye da haka, sai ya ce: To sai a ba shi aminci a damarsa da dawwama a hagunsa sannan sai ya shiga aljanna ana mai ce masa: Karanta (aya daga cikin ayoyi) darajarka da daukakarka su kara dagawa sama. Sannan sai a ce wa Qur'ani shin mun gamsar da kai game da shi? Sai Qur'ani ya ce: Eh na gamsu[4].
Da wadansu fa’idodin masu yawa. Duba ka ga yadda wasu fa’idodin ba su takaita ga musulmai kawai ba, shi ya sa za ka ga irin yadda mufakkirai, masana da jagorori suke rige-rigen riko da Qur'anin nan koda ba su kasance musulmai ba.
Zuwa nan dan abin da na kawo na karfafar gwiwa zai iya wadatarwa ga mutum ya kama hanya, ya motsa, sannan kuma ya yunkura wajen ganin ya rungumi wannan Littafi mai karamci ya girmama shi ta yadda zai wayi gari ya cakude da jinin jikinsa da tsokarsa. Don haka ni yanzu a nan ina mai lizimta[5] maku cewa duk wanda yake ganin ina da wani matsayi a wajensa shin matsayin nan na akhlak ne ko na shari'a to ya dinga saukar Qur'ani mafi karanci sau biyu a shekara. Wannan kau ba wani abu ne mai yawa ba musamman idan muka kalli watan Ramadan wanda a cikinsa kadai ma mutum zai iya yin sauka daya da rabi ta Qur'ani ko ma fiye.
Amma mafi muhimmanci na daga abin da na ambata na karfafar gwiwa su ne abubuwan da aka rawaito daga madaukakan hadisai wadanda na zabo maku wasu daga cikinsu adadinsu zai dan wuce arba’in wanda yake wata Sunnah ce mai gudana a tsakanin malamai magabata mutanen kwarai, wadanda suka wallafa da yawa daga cikin littafai masu suna (Al-arba’una Hadisa – wato Hadisai Arba’in) a fagage daban-daban na ma’arifa da ilimi, ina fatan su zamanto kuma ni ma na zamanto tare da su cikin masu aiki kuma ma’abota wannan madaukakin hadisi, wanda a cikinsa Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: “Wanda ya haddace daga gare ni daga cikin al'ummata hadisi arba’in a cikin al’amarin addininsa yana neman yardar Allah da wannan da kuma ranara lahira, Allah zai tashe shi a ranar kiyama faqihi malami”[6].
[1] Al-Kafi: 2/609.
[2] Sunanul Darami: 2/435, Kitabu Fada’ilil Qur'an, da irin hadisin a cikin kebantattun littafai; (littafan shi’a).
[3] An ambace shi a cikin Al-Mizan wanda ya zo a cikin wasu littafan; mujalladi na 3, a karkashin tafsirin aya ta 7-9 cikin suratu Aali Imran.
[4] Al-Kafi: 2/604.
[5] Wannan lizimtawar ta karfafi da yawa wadanda suka ta shi tsaye wajen aiwatar da ita, da fatan Allah ya yi masu kyakkyawan sakamakon da yake yi wa masu kyautatawa.
[6] Al-Khisal: 2/542, babin (Al-Arba’un).