Muhimmantarwar Annabi (S.A.W.A) Da Ahlul Baiti (As) Ga Qur'ani

| |times read : 334
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Muhimmantarwar Annabi (S.A.W.A) Da Ahlul Baiti (As) Ga Qur'ani

        Muhimmantarwar Annabi (s.a.w.a) da Ahlul Baiti (as) ga Qur'ani ta kai kololuwa matuka gaya, akwai ruwaya ma da aka samo daga Imam Sajjad (as) yana cewa: “Da mutanen gabas da yamma za su mutu ba zan taba yin ko gezau ba matukar Qur'ani yana tare da ni”[1].

Lallai an umarci Manzon Allah (s.a.w.a) da yin tilawar Qur'ani: “Kuma ka kyautata tilawar Qur'ani, daki-daki” Muzzammil: 4. Kuma Allah tabaraka wa Ta'ala ya sake umartarsa da ya lizimci sallatar sallolin nafila na dare domin ya samu shiri na musamman na isar da saqon musulunci inda Allah Ta'ala din ya ce: “Lallai ne mu, za mu jefa maka magana mai nauyi. Lallai ne tashin tsakar dare yana haifar da tsananin natsuwa, kuma mafi daidaituwa ga magana” Muzzammil 5-6. Manzon Allah (s.a.w.a) bai wadatu kawai da karanta shi ba, a’a yana neman Abdullah ibn Mas’ud da ya karanta masa, har ma yakan nemi uzuri a wajen Manzon Allah (s.a.w.a) yana mai fadin: Kai fa aka saukarwa da shi ya Rasulallah amma kuma kana neman ka ji shi daga wajena? To sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce masa: Ina son in ji shi daga gare ka. To sai Abdullah ya karanta, sai idanun Manzon Allah (s.a.w.a) su cika da kwalla”. Hakan da yake yi yana bukatar dukkan sasannin jikinsa su samu sakina da ainahin shi Qur'anin, tun daga idanuwansa, kunnuwansa, zuciyarsa zuwa harshensa, kuma yasan cewa kowace gabar jiki tana da hanyar da take samun masaniya to sai ya kwadaici – tare da cewa shi ne mafi kamalar halittu – kowadanne sassan jikin nasa su isa ga kamala. Akwai wani hadisi da ya zo wanda ma’anarsa tana cewa ne duk wanda ya rasa ji - (ji na daya daga cikin gabbai guda biyar) – to hakika ya rasa ilimi, to sai ya so ya amfana da ilimummukan Qur'ani ta hanyar gabaki dayan gabban jikinsa. A dalili da haka ne ma ya zo cewa mustahabbi ne a karanta Qur'ani da sauti mai dadin ji.

Wannan ban da abin da ya zo game da falala da ladar sauraren karatun Qur'ani da duba ga shafukansa a yayin karantawa koda kuwa ya haddace abin da yake karantawa din, kuma koda a sallah ne, bayanin da da sannu zai zo da izinin Allah Ta'ala a cikin tarin hadisai masu zuwa nan gaba.

Kuma yanayin mu’amalar Manzon Allah (s.a.w.a) da Qur'ani ta kasance yakan karanta wa sahabbansa, wata rana ya karanta masu suratul Rahman suka zauna suna saurare, sai (s.a.w.a) ya ce: Hakika na karantata ga aljannu, to kuma sun kasance sun fi ku kyautata saurare, sai suka ce ya Manzon Allah (s.a.w.a) ya aka yi haka? Sai ya ce: Sun kasance duk lokacin da na karanta: “To saboda wadanne daga ni’imomin Ubangijinku kuke karyatawa”? Sai sukan ce: Babu wani abu daga ni’imomin Ubangijinmu da muke karyatawa. Idan kuma ya karanta fadin Allah Ta'ala: “Ashe wannan (wanda ya yi irin wannan halitta) bai zama mai iko a kan rayar da matattu ba”. Manzon Allah (s.a.w.a) yakan ce: Haka yake tsarki ya tabbata a gare ka ya Allah, domin ya kasance yana ji kai tsaye daga wajen Allah Tabaraka wa Ta'ala ba da shamaki ba. Da sannu zai zo daga Imam Kazim (as) ya kasance yana karantawa kai ka ce yana yiwa wani mutum magana ne. Manzon Allah (s.a.w.a) ya karanta surar Zumar ga wani matashi mai tsarkakakkiyar zuciya, mai tsarkin makwanci a lokacin da ya isa ga fadin Allah Ta'ala: “Kuma aka kora wadanda suka kafirta zuwa jahannama, jama’a-jama’a”, Zumar: 71. Da fadinsa Ta’ala: “Kuma aka kora wadanda suka bi Ubangijinsu da takawa zuwa aljanna jama’a-jama’a”, Zumar: 73. Sai matashin nan ya yi wata kara, kara mai motsa rai, sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya karanta surar Hal ata alal insani hinun minal dahari (Lallai ne wata mudda ta zamani ta zo a kan mutum (a yayin da) bai kasance komai abin ambato ba). Ta sauka ne a gare shi a lokacin da yake tare da wani mutum bakar fata, amma a lokacin da ya isa ga ayoyin da suke siffanta aljanna sai ya numfasa numfasawa kawai sai ransa ya fice, sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: “Ran abokinku ya fita saboda kwadayinsa ga aljanna, irin wadannan ayar Qur'ani ta siffanta su da: “Wadanda muka baiwa Littafi suna karatunsa hakikanin karatunsa, wadannan su ne ke yin imani da shi (Qur'anin), kuma wanda ya kafirta da shi, to wadannan su ne masu asara” Bakara: 121.  



[1] Al-Kafi: 2/602.