Bukatarmu Ta A Sake Raya Qur'ani
Bukatarmu Ta A Sake Raya Qur'ani
Muna da bukata ta sake dawo da tasirin Qur'ani a cikin rayuwar musulmi, da fitar da shi a cikin wannan marrar da ya samu kansa a ciki, ta yadda samuwarsa ta takaitu kawai a cikin tarurrukan ta’aziyya da zaman gaisuwar mamatanmu da wuraren wa’azi.
Alhali ya zo a cikin wasu kalmomi cewa: “Karshen wannan al'umma ba zai gyaru ba sai da abin da ya gyara na farkonta”. Kuma lallai al'ummar farko sun gyaru ne ta hanyar Qur'ani, don haka idan al'umma tana bukatar ta taimaka ta inganta rayuwarta sannan ta koma zuwa ga daukakarta to sai ta koma wa Qur'ani. An samu daga Mikdad (r.a) daga Manzon Allah (s.a.w.a) a cikin wani hadisi ya ce: “Idan fitintinu suka rikirkice maku, kamar wani yankin dare mai tsananin duhu, to na hore ku da ku kama Qur'ani, domin shi waraka ne mai warkarwa, mai tattaunawa ne da gaskiya, duk wanda ya sanya shi a gaba gare shi zai jagoran ce shi zuwa aljanna, wanda duk ya saka shi a bayansa sai iza keyarsa zuwa wuta, domin shi dalili ne da yake nuni a kan alheri”[1]. Amirul Muminina (as) a cikin wata hudubarsa ya ce: “Ku sani lallai wannan Qur'ani mai nasiha ne wanda ba ya algushu, mai shiryarwar da ba ya batarwa, mai bayar da labarin da ba ya karya, babu wanda zai zauna da Qur'ani sai ya karu da shi ko ya ragu; karuwa a cikin shiriya, ita kuma raguwa daga makanta, ku sani babu talauci ga wanda yake tare da Qur'ani, kamar yadda babu arziki da shiriya ga wanda ya juya wa Qur'ani baya, don haka ku nemi waraka daga gare shi na cutukanku kuma ku nemi taimakonsa domin a cikinsa akwai waraka na mafi girman cuta (cutuka kau mafi girma) su ne kafirci, munafurci da bata, saboda haka ku roki Allah don alfarmar Qur'ani ku karkata zuwa gare shi da kaunarsa, kada ku tambayi ababen halitta da shi domin bayi ba su karkata ga Allah da wani abu kamarsa ba. Ku sani cewa shi waraka ne mai warkarwa, mai jayayyane da gaskiya, kuma lallai duk wanda Qur'ani ya ceta a ranar kiyama, to ta gaskata a kansa, domin mai kira zai yi kira a ranar kiyama: “Ku saurara! Duk wani manomi an jarabce shi game da nomansa da ayyukansa da ya aikata in banda ayyukansa da suka dace da koyarwar Qur'ani, don haka ku zamo cikin wadanda suke aiki da koyarwarsa, masu biyayya gare shi, ku nemi sanin Allah ta hanyarsa, ku yi wa kawukanku nasiha da shi, ku tuhumci kawukanku idan suka sabawa ra’ayin Qur'ani da soyace-soyacen rayukanku marasa kyau”[2].
[1] Al-Kafi: 2/299.
[2] Nahajul Balaga, Sharhin Muhammad Abduh, 1/347, huduba ta 177, wacce farkonta ya fara da: {Ku amfanar da kawukanku da bayanan Allah, kuma ku wa’aztu da wa’azinsa}.