Qur'ani Shi Ne Hanyar Isa Ga Sanin Allah Tabaraka Wa Ta'ala
Qur'ani Shi Ne Hanyar Isa Ga Sanin Allah Tabaraka Wa Ta'ala
Duk wanda ya nufi Allah Subhanahu kuma yake neman isa gare shi, kamar yadda ya zo cewa farkon addini saninsa Ta’ala, to ya lizimci Qur'ani domin (Lallai Allah ya yi tajalli ga bayinsa a cikin zancensa, sai dai ba su gani)[1]. Kamar yadda aka rawaito daga Imam Sadik (as): Duk wanda yake son ya gyara zuciyarsa ya tsarkake ta da taskace ta daga dukkan cututtuka to ya lizimci Qur'ani, haka nan wanda yake son gyara al'ummarsa da tsayuwar lamurranta cikin aminci da dacewa da natsuwa, to ya lizimci Qur'ani domin shi ne dalili na dukkan shiriya mai shiryatarwa ga dukkan alheri da gyara.
Wani abin al’ajabi shi ne cewa da zarar wani inji ya lalace, kai tsaye za ka tafi gurin masanan wannan injin domin su gyara maka, domin su masu gyaran nan suna da masaniya ciki da bai a kansa, kuma da rashin lafiya za ta same ka – Allah ya tsare – za ka tafi wajen kwararren likita domin ya duba ka ya ba ka magani, amma kuma lokacin da kake son ka gyara zuciyar dan adam wacce ke dauke da cakudaddun boyayyun sirruka hatta ga mamallakinta ballantana kuma waninsa, ko yayin da kake son kawo wa mutane wani tsari wanda zai dauki nauyin daidaita masu rayuwarsu da ci gabansu, kwatsam sai ka fara neman kamun kafa a wajen shi dai ainahin mutum wanda yake gajiyayye, nakasasshe kuma rarrauna. Ba za ka tafi wajen wanda ya samar da shi mutum din, ya halittashi, ya saita halittarsa kuma ya san sirrin zuciyarsa ciki da bai dinta ba.
Kuma lallai tajruba mai girma ta Manzon Allah (s.a.w.a) ta gaskata wannan – wato rawar da Qur'ani ya taka wajen gyaran zukata da zamantakewar al'umma – wanda da a ce za a dan kwatanta kadan tsakanin al'ummar kafin zuwan musulunci da al'ummar bayan zuwansa da an ga irin babban canjin da ya faru ga wadannan jahilan mutanen wadanda suke a warwatse, suna rayuwa cikin munanan dabi’u, dabi’un da suke a tarwatse a tsakaninsu har suna alfahari da munanan ayyuka da ababen ki, amma suka canza zuwa wata al’umma mai wayewa da ci gaba, mai karamci, ma’abociyar tsari da nizami, abin da kafin wannan lokaci ba a samu wata al'umma wacce ba ta san Allah ba, ta ga makamancin irin wannan canjin, musamman ma irin gyaran da aka samu a dan kankanin lokaci, wanda kuma duk albarkacin samuwar wannan Littafin mai girma ne da wadanda suke dauke da shi masu girma.
[1] Awalil Li’ali: 4/116.