WASICI DA YIN HADDAR QUR'ANI
WASICI DA YIN HADDAR QUR'ANI
Kada ikirarin wadancan mutanen ya rudar da ku cewa su ne masu lazimtar Qur'ani fiye da mu[1]. Ku haddace Qur'ani domin shi ahalin haka din ne, tare da yin aiki da shi, ku zama kamar yadda Amirul Muminina (as) ya yi wasicci a kai a gab da shahadarsa: “Na gama ku da Allah! Na gama ku da Allah! Game da Qur'ani kada ku bari waninku ya shiga gabanku a wajen yin aiki da shi”[2]. A cikin wasiyyar Annabi (s.a.w.a) ga Amirul Muminina (as) ga yin aiki da hadisai arba’in ya ce: “Kuma ka yawaita da yin aiki da abin da ke cikinsa”[3].
[1] Kuma na kara nanata wannan lamari domin ana yaudarar da yawa daga wawayen mutane da aka yi ta wannan hanyar na cewa sun fi mu lazimtar Qur'ani, har suka kai sun fara yarda da gaskata su ta hanyar kin yin imani da duk wani abu sai idan an samu dalilinsa daga Qur'ani suna wurgar da kowane dalili da aka samu daga sunna.
[2] Biharul Anwar: 42/256.
[3] Al-Khisal: Abwabul Arba’in, hadisi na 19.