Bai Yi Riko Da Qur'ani Ba Wanda Ya Juya Wa Ahlul Baiti (As) Baya
Bai Yi Riko Da Qur'ani Ba Wanda Ya Juya Wa Ahlul Baiti (As) Baya
Amma sai muka samu al'umma ta bar Qur'ani ta nisanta kanta daga gare shi tun lokacin da ta kawar da iyalan gidan Annabta daga matsayinsu wanda Allah Subhanahu wa Ta’ala ya zabar masu, don raba su da Qur'ani ba abu ne da zai yiwu ba, suna masu bijirewa fadin Allah Ta'ala: “Kuma Ubangijinka yana halitta abin da yake so, kuma shi ke yin zabi, zabi bai kasance a gare su ba”, Qasas: 68.
Kuma yana daga cikin yasassar magana da ingiza mai kantu ruwan shaidan da tinkahon rai mai yawan umarni da mummunan aiki wani mai magana ya zo ya ce: (Littafin Allah ya ishe mu <Hasbuna Kitabullah>) zancen da har yanzu ba su gushe ba suna maimaita shi, kuma shaidan yana furta shi daga harshen wanda yake neman ganin rugujewar ginin musulunci tun daga tushensa, wanda daga cikinsu har da shi Qur'anin wanda mai maganar yake ikirarin cewa ya ishe shi, domin ko ya sani sarai cewa shi Qur'anin yana iya tsayuwa kyam a kan aikinsa ne kawai har kuma ya iya samun damar taka rawarsa idan an gwama shi da masu tsayar da dokokinsa da ilimummukan da ke cikinsa wadanda kuma su ne iyalan gidan Annabta.
Wannan fitinar – ta shiga tsakanin Qur'ani da masu magana da yawunsa – tsohuwar fitina ce da Amirul Muminina (as) yana daga cikin wadanda aka jarabce su da ita, lokacin da aka tilasta masa hukunci cewa dole Qur'ani ya zama shi ne mai shiga tsakani, sai Imam (as) ya ce: “Shi Qur'anin nan ba wani abu ba ne face rubutu wanda aka taskace a tsakanin bangwaye guda biyu, shi a kashin kansa ba ya magana da baki, saboda haka dole ne yana bukatar wanda zai yi magana tare da fassara shi, kuma masana su ne kawai za su iya magana da yawunsa”[1].
Don haka da Littafi da iyalan gidan Annabta wadansu abubuwa biyu ne da ba za su taba rabuwa da juna ba, kuma ba zi yiwu a yi riko da dayansu a kyale daya ba, domin su Ahlul Bait (as) kofar Allah ce wacce ba a je masa sai ta wannan kofar kamar dai yadda ya umarce mu da mu je wa gidaje ta kofofinsu.
A saboda haka duk wani wanda ya yi ikirarin cewa ya damu da Qur'ani fiye da mu tabbas zancensa batacce ne, eh sun mayar da hankali ga yadda ake fitar da haruffa, kyautata sauti har zuwa ga tangimi a wajen karantawa, rikodin dinsa da ka’idojin tajwidi wadanda su da kansu suka sanya su, wasunsu ma sun sabawa shari'a, wadannan dukkansu wasu nau’oin kulawa ce marar muhimmanci, abin da yake mai muhimmanci shi ne fahimtar abin da ke cikinnsa da abin da ya kunsa da yin aiki da shi, domin lafazi ba komai ba ne face bawo, ma’ana ita ce ainahin tsokar da ake bukata, kuma shi mai magana ba ya lura ga lafazi a kan kansa, a’a yana daukar lafazi ne a matsayin mazubi da wani tsani na ma’ana wanda zai isar da shi ga wanda yake wa magana, kuma ita ma'ana ita ce ainahin abin nufi na hakika ga mai magana.
An samu hadisai masu yawa sun zo suna sukar masu wasa da lafuzzan Qur'ani da haruffansa, masu batar da ma'anoninsa da iyakokinsa, an samu a cikin wani hadisi mash’huri: “Za ka samu daga cikin masu karanta Qur'ani, amma Qur'anin yana la’antarsu”[2]. Yana husuma da shi domin ba ya aiki da abin da ke cikinsa. A cikin wani hadisi daga Abu Ja’afar (as) ya ce: “Makaranta Qur'ani kashi uku ne: Mutumin da ya karanta Qur'ani amma sai ya dauke shi haja ya kewaya da shi a fadar masu mulki, ya tsananta shi a kan jama’a, to wannan yana daga cikin ‘yan wuta, wani mutumin kuma ya karanta Qur'ani ya haddace haruffansa amma ya keta dokokinsa to wannan shi ma yana daga cikin ‘yan wuta, wani mutumin kuma ya karanta Qur'ani sai ya sanya shi a matsayin maganin da yake warkar da rashin lafiyar zuciyarsa, ya dinga debe kewa da shi yana cinye dare cikin karanta shi, ya kosar da kishin ruwansa da shi a yininsa, ya tsayu da shi a masallatai kuma sasanninsa suna nisanta daga wuraren kwanciya domin karanta shi, to da wadannan ne Allah yake kwabe bala’oi da kuma da su ne yake ba da nasara a kan makiya – ai yana taimakon su a kan makiyansu – kuma da su ne yake saukar da ruwan sama, na rantse da Allah wadannan makaranta Qur'anin sun fi kibritil ahmar[3] kima da daraja”[4]. A wani hadisi daga Imam Hasan (as) ya ce: “Lallai mafi cancanta da Qur'ani shi ne wanda ya yi aiki da shi koda bai haddace shi ba, wanda yafi nisantarsa kuma shi ne wanda ba ya aiki da shi koda yana karanta shi”[5].
Daga nan za mu gane cewa makircin raba tsakanin Qur'ani da iyalan gidan Annabta, tare da zare karantarwar Littafin da abubuwan da ya kunsa aka barshi fankam fayau aka karfafi muhimmatar da lafuzzansa cewa wani tsohon makirci ne, kuma Ma’asumai (as) sun yi gargadi; to wai ma mene ne za a kira muhimmantarwar alhalin ga aya tana cewa: “Kuma Ubangijinka yana halitta abin da yake so, kuma shi ke yin zabi, zabi bai kasance a gare su ba”, Qasas: 68. Sannan ya bijirewa wadanda Allah Ta'ala ya zaba da kansa, ya gabatar da wasunsu, alhali Allah Ta'ala ya riga ya sanya wannan al’amarin gabaki dayansa a tafin hannun saqon musulunci shi kuma saqon gaba dayansa a daya tafin hannun inda Allah ya ce: “Ya kai Manzo! Ka iyar da abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka, kuma idan ba ka aikata hakan ba, to ba ka iyar da manzancinsa ba kenan, kuma Allah yana tsare ka daga mutane”, Ma’ida: 67.
Wace irin biyayya ce ake wa Qur'anin wanda shi Qur'anin yake cewa da madaukakin sautinsa: “Ka ce: Ba na tambayarku wata lada a kansa, face nuna soyayya da kauna ga makusantana”, Shura: 23. Alhali suna bayyana kiyayya ga Ahlul Baitin gidan Annabta, suna farautarsu a karkashin kowane dutse da marmara, da a ce suna da mafi karancin fahimta ta Qur'ani da sun gwama ma'anar wannan ayar da wacce ta gabace ta zwa inda Allah ke cewa: “Kace: Ba na tambayarku wata lada a kansa, face duk wanda ya so to ya riki hanya zuwa ga Ubangijinsa” Furkan: 57. Da sun kai ga gane hakika cewa lallai Ahlul Baiti su ne hanyar nan da Allah Ta'ala ya yi umari a bi a cikin fadinsa: “Kuma lallai wannan ne tafarkina madaidaici, sai ku bi shi, kuma kada ku bi wasu hanyoyi, su rarraba ku daga barin hanyata, wannan ne Allah ya yi maku wasiyya da shi ko kun yi takawa”, An’am: 153. Da wannan ne Imam Baqir (as) ya yi tafsirin ayar da cewa: “Mu ne hanyar, kuma duk wanda ya qi bin wannan hanyar hakika ya kafirta”[6].
Ni ba zan ce kalmar (hasbuna kitabullah = Littafin Allah ya ishe mu) da amsa-amon da yake tare da ita, suna ta maimaitata har zuwa yau din nan, suna kuma neman dalili daga Qur'ani kadai, wai a kan mene ne a ke fada masu wai ita kalma ce ta gaskiya da aka nemi bata da ita, a’a ai ita kanta kalmar kalma ce ta bata da aka nemi bata da ita. Kuma su wadannan ba wani abu suke nema da wannan ba sai ruguje tushen addini, domin wadatuwa da Qur'ani kadai – kamar yadda suke riyawa – yana nufin wadatuwarsu hatta ga barin Manzon Allah (s.a.w.a) wanda hakan yake nufin jahilci tsantsa da cikakkiyar ma’anarsa, domin Manzon Allah (s.a.w.a) da alayensa Imamai Ma’asumai (as) su ne masu tsayuwa da al’amarin Littafin da yin bayanin hukunce-hukuncen da ke cikinsa.
Duba ka gani ga ilimummuka nan a gabanka na kimiyya, shin kana ganin za ka iya zama likita ko injiniya ba tare da ka koya daga kwararru masanan sirrin ilimin, ciki da bai dinsa ba? To me ya sa sai Qur'ani wanda yake shi mai: “Yin bayani ne ga dukkan komai”. Nahl: 89. Da kuma ayar: “Ba abin da muka bari ba mu yi bayaninsa ba a Littafi” An’am: 38. Kuma a cikinsa akwai duk wata maslahar ‘yan adamtaka a kowane zamani. Allah ya ce: “Me ya same ku, wane irin hukunci ne haka ku ke yi!” Saffat: 154. Kuma Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi gargadi game da wannan hadarin inda ya ce: “Kada dai in samu dayanku, ya kishingida gadon bayansa a kan karaga yana hutawa, sai a zo masa da tambaya kan wani lamari daga cikin lamurrana da na riga na yi maku bayaninsa, amma sai ya ce: ban sani ba, ba mu ga wannan a cikin littafin Allah wanda muke bi ba”[7].
Sai dai makiya Allah Ta'ala kuma mabiya shaidan sun sani sarai cewa wannan Qur'anin shi ne garkuwar wannan al’ummar kuma mai ba ta kariya daga rushewa da sakin hanya, kuma Ahlul Baiti (as) su ne masu tsayuwa da shi, don haka sai suka kitsa yadda za su nesanta su daga mutane, don haka sai al'umma ta wayi gari ta rasa garkuwa da makiyayi da mai ba ta kariya. Har al'umma ta wayi gari ta zama sassaukar ganima a hannun makiya da masu jiran ganinta cikin mummunan hali.
Duba ka ga yadda a sakamakon ‘yar kankanuwar shubuha sai al'umma ta kama makyarkyata, tana rushewa sakamakon ‘yar fitina kyas, tana faduwa saboda ‘yar jarabawa ‘yar karama ((wannan kuma shi ne mafi girman gibin da aka yi wa ilimin Qur'ani, da toshe kafar yin tunani ko tunatarwar da za su iya wani tasiri, kuma daga cikin abin da yake shaida samuwar wannan matsalar shi ne karancin samun hadisan da za a ce an rawaito daga Imamai (as), idan ka yi tunani a kan abin da ilimin hadisi a zamanin kalifofi yake dauke da su na matsayai da karamomi da kuma halin da mutane suka kasance a ciki na kwadayi mai tsanani na karbar hadisan sannan ka lissafa abin da aka nakalto daga cikinsa daga Ali (as), Hasan da Husain (as) musamman ma abin da aka nakalto wanda ya shafi tafsirin Qur'ani da ka ga abin mamaki: Domin sahabbai ba su nakalto wani abin ambato daga Ali (as) ba, amma su tabi’ai abin da suka nakalto daga gare shi – idan dai lissafawa za a yi – ba za su wuce ruwayoyi dari ba a gabaki dayan tafsirin Qur'ani, shi ma Hasan (as) dan abin da aka nakalto daga gare shi ba ya wuce goma, shi kuma Husain (as) babu wani abu da za a ce ga shi an nakalto daga gare shi, amma wasunsu sun gama tattara ruwayoyi na tafsiri har guda dubu goma sha bakwai (Suyudi ya ambaci wannan a cikin Al-Itqan) wadanda hadisai ne da suka zo ta bangaren ahlul Sunnah su kadai, kuma za ka samu kwatankwacin wannan a ruwayoyin fikihu))[8].
Me ya fi wannan zama asara ga Qur'ani kamar irin nisanta Ahlul Baiti (as) da aka yi daga taka rawarsu da sauke nauyin da ke kansu, alhali Allah Ta'ala ya zabe su domin su yi hakan!
1- Bacewar da yawa daga cikin ilimummuka na hakika wadanda babu wani wanda zai iya fahimtarsu daga Littafi sai su kawai (as).
2- Ja da bayan da Qur'ani ya yi wajen taka tasa rawar domin gyaran zukata da al'umma, domin shi da iyalan gidan Annabta ma’aunai ne guda biyu da ba su rabuwa, kuma ba zai yiwu ya zama ya tsayu da ayyukansa ba dole sai da su.
3- Fadawar da Qur'ani ya yi ya zama abin farauta a hannun masu wasa da shi da masu biyewa son zukatansu da bukatun kashin kai, kai har da ma makiya kuma, ta yadda za ka ga kowanne daga cikinsu yana samarwa kansa dalili na akidarsa daga Littafin Allah. Hatta Kawarijawa sun kasance suna kafa dalili da Qur'ani kamar yadda yayin da wani hukunci ya shiga tsakaninsu da ibn Abbas, sai Ali (as) ya hane shi da kafa hujja da Qur'ani, domin shi Qur'ani (yana daukar fuskoki biyu)[9]. Ma’anoninsa na hakika suka zama abin layya wadanda ake masu tawiloli, kuma Qur'ani din da kansa ya yi gargadi a kan hakan: “To amma wadanda suke a cikin zukatansu akwai karkata, sai su dinga bin abin da yake da kama da juna daga gare shi, domin neman yin fitina da tawilinsa”, sai da amsar a fili take, kuma Qur'ani ya bayar da ita a gaba cewa: “Kuma babu wanda ya san tawilinsa face Allah da kuma matabbata a cikin ilimi”, Aali Imran: 7. Mafi bayyanar misdakin matabbata a cikin ilimi su ne Ahlul Baiti (as).
4- Tarwatsewar al’umma, rugurgujewarsu da yamutsewarsu sakamakon gujewa masu ba su kariya kuma masu tattarasu wato Qur'ani da Ahlul Baiti kamar yadda tafsirin Manzon Allah (s.a.w.a) ga wannan ayar ya nuna a cikin fadinsa Ta’ala: “Kuma ku yi riko da igiyar Allah gabaki daya kuma kada ku rarraba”, Aali Imran: 103. Sai Annabi (s.a.w.a) ya ce: Su ne Littafin Allah da iyalan gidan Annabta. Kuma lallai Sayyida Fatima Al-Zahra (as) game da wannan kiyayewar a cikin hudubarta a cikin masallacin Manzon Allah (s.a.w.a) ta ce: Allah ya sanya Imamancinmu nizami da tsari domin al'umma”[10].
Ai da wannan din ne al’marin al'umma zai tsayu ya kafu, a saboda haka ne nisantarsu ga Ahlul Baiti ta haifar masu da fadawa hannun mabarnata masu salladuwa a kansu, masu bautar soyace-soyacen rayukansu, wadanda suka yi amfani da wannan damar ta watsar da Qur'ani da twagwayensa da aka yi suka hallakar da komai hatta shuka da ‘ya’yan dabbobi ba su bari ba. Kuma ya kasance daga cikin (wa’azin wadannan mabarnatan) da masu tarayya da su a cikin barna cikin irin wadanda suke halatta masu wadannan munanan ayyukan nasu, kamar fadinsa Ta’ala: “Ku yi da’a ga Allah, kuma ku yi da’a ga Manzonsa da majibinta al’amari daga cikinku” Nisa’i: 59. To amma sai suka sanya kafiran fasikai a matsayin majibinta al’amari ga al’amurran musulmai.
[1] Nahjul Balaga: Huduba ta 125.
[2] Mustadrakul Wasa’il: Kitabul Salat, babukan karanta Qur'ani, babi na 7, hadisi na 7.
[3] Wani abu ne mai kima da daraja wanda hadisai da ruwayoyi sukan yawaita kawo misali da shi.
[4] Al-Khisal: 142.
[5] Irshadul Qulub: 79.
[6] Biharul Anwar 13/24, babin: Cewa su Imamai (as) su ne hanya kuma su ne tafarki tare da shi’arsu.
[7] Al-Mizan Fi Tafsiril Qur'an: mujalladi na 3, a bangaren bahasin ruwayoyi na aya ta 28-32 cikin suratul Aali Imran, Ahmad, Abu Dawud, Tirmizi, Bn Maja, Bn Hibban da saurasu su ne suka ruwaito shi, wadannan duk cikarsu maruwaitan suna daga bangaren ‘yan uwa ahlul Sunnah ne.
[8] Al-Mizan Fi Tafsiril Qur'an: mujalladi na 5, a bangaren bahasin tarihi a karkashin aya ta 15-19 a cikin suratul Ma’ida.
[9] Biharul Anwar: 2/245.
[10] Kashful Gumma: 2/110.