Nisantar Da Aka Yi Wa Qur'ani Shi Ne Sababin Raunin Musulmai
Nisantar Da Aka Yi Wa Qur'ani Shi Ne Sababin Raunin Musulmai
Lallai zabar yin magana game da wannan korafin da koken ba kawai ya zo ne haka siddan ba, ba kuma yawaitar tunani ne ya sa ba, a’a ya samo asali ne daga basira da tunani mai zurfi da nazari mai kyau a yayin bincike da tantance hakikanin al’ummar musulmi wadanda yanayin halin zamantakewarsu ya zama suna cikin taraddudi, har ta kai su ga suna yin kyauta ga wanda ya kashe masu wanda suke kallo a matsayin makiyi a gare su, alhali hakikanin makiyansu su ne ibilis, ransu mai umarni ga mummunan aiki da kuma ma’abota girman kai[1] da abubuwan da ta sana’anta na yankin kafirci na yammacin turai wanda ya himmantu wajen ganin ya kawo rarraba tsakanin musulmai da sirrin karfinsu da izzarsu, sharafinsu da karamcinsu wanda yake shi ne Qur'ani, alhali yanzu ya zama shi bako ne a tsakaninsu, wannan ne ya janyo wata damuwa ta tsaya min ta yi min katutu a zuciyata.
Lallai sabubban gazawa da rugujewar al'umma da koma bayan da ta samu kanta a ciki na rauni sun samu ne sakamakon barin rikonsu ga igiyar Allah Ta'ala, bayan Allah din ya umarce su da su yi riko da ita. Allah Ta'ala yana cewa: “Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya, kuma kada ku rarraba”, Aali Imran: 103. Sannan lallai Manzon Allah (s.a.w.a) ya bayyana mece ce wannan igiyar a inda ya ce: “Kuma ni mai bar maku sakalain ne (nauyaya guda biyu) a bayana; Nauyi mafi girma shi ne Qur'ani, karamin nauyin kuma su ne alayena wato Ahlul Bait dina; su biyun nan su ne igiyar Allah mikakkiya a tsakaninku da tsakanin Allah Azza wa Jalla, madamar ku ka yi riko da su ba za ku bata ba, wani sababi daga gare ta a hannun Allah yake wani sababin kuma a hannunku yake….”. Wannan hadisin[2].
[1] Ana jingina kalmar girman kai ga wasu majmu’a ma’abota karfin siyasa, sojoji, ilimi da tattalin arziki, wadanda suke dogaro ga wata nazariyyar mai bambance dan adam zuwa mataki-mataki, sai kuma suna yin amfani da wani tsari mai girma – wato jama’a, hukuma da kasa – sai su doru a kansu suna masu salladuwa a kansu a wani yanayi abin takaici da wulakanci. Suna kutsawa cikin sha’anoninsu, suna kwashe dukiyoyinsu, suna amfani da hukumominsu ta hanyar nuna karfi da isa, suna zaluntar ‘yan kasa, suna yin hawan kawara ga al’adunsu da akidunsu.
[2] Biharul Anwar: 92/102