KORAFIN AL-QUR’ANI
KORAFIN AL-QUR’ANI
Hakika na zabi na fara da hadisi mai girma wanda aka rawaito a cikin littafin Al-Kafi da Al-Khisal daga Abu Abdullah (as) ya ce: “Abubuwa guda uku suna kai kukansu da korafinsu ga Allah Azza wa Jalla; masallacin da aka yasar da shi ya lalace mutanen unguwa ba su shiga yin sallah a cikinsa; malamin da yake zaune a tsakanin jahilai sai Mus’hafin (Qur'anin) da aka rataye shi kura ta turbude shi ba’a karanta komai na cikinsa)[1].
Kuma misdaki mafi bayyana idan ana maganar malami, su ne Ahlul Bait (as) musamman ma Imamin wannan zamanin mai tsayuwa da al’amari (rayukanmu su zama fansa gare shi). A saboda haka wadannan ukun da za su kai kara da korafi su ne Qur'ani, iyalan gidan Annabta da kuma masallaci. Wani hadisin da aka rawaito daga Annabi (s.a.w.a) yana nuni a kan haka yayin da ya ce: “Abubuwa uku za su zo ranar alkiyama suna masu kai kokensu: Mushafi, masallaci da iyalan gidan Annabta, Mus’hafi zai ce ya Ubangijina! Sun jirkitani kuma sun cukurkudani, shi kuma masalllaci zai ce: Ya Ubangijina! Sun kau da kai ga barina kuma sun wulakantani, su kuma iyalan gidan Annabta za su ce: Ya Ubangiji! Sun kashe mu kisan gilla, sun kore mu kuma sun raba mu da garuruwanmu. Don haka ku zama cikin shirin tuhuma a gobe kiyama, a daidai wannan lokacin Allah Azza wa Jalla zai ce min: Ni ne na fi ka cancantar bin hakkin wadannan ukun”[2].
Za mu iya amfana da wannan hadisin a wurare da yawa:
Na Farko: Lallai asasin gini na wannan al’ummar ta musulunci da abubuwan da za su karfafi matsugunnin jama’ar musulmi su ne wadannan rukunnan guda uku, saboda haka ne ma aka mayar da hankali gare su, kuma magana a kan wannan tana komawa ga ma’anar shahararren hadisin nan na sakalaini mai cewa: “Ni mai bar maku nauyaya guda biyu ne: Littafin Allah da alayena iyalan gidana, madamar ku ka yi riko da su, a bayana ba za ku taba bata ba har abada, lallai mai bayar da labari ya fada min cewa tabbas wadannan biyun ba za su rabu ba har sai sun same ni a tabki a ranar kiyama”[3]. Wadannan sakalaini din su ne biyun ukun can, amma na ukun wanda yake shi ne masallaci shi wani mahalli ne da su sakalaini din suke isar da karantarwarsu a cikinsa wanda suke a unguwanni wato wuraren da al’umma suke tare da samar da alakoki a cikin farfajiyarsa mai tsarki.
Na Biyu: Alamu wadanda suke nuna cewa al’umma za ta juya wa wadannan ukun baya, za ta mayar da su a can bayan-bayanta, a dalilin haka ne ma (Annabi (s.a.w.a)) ya ba da labari na koke da korafin da za su yi a matsayin wani abu na hakika da zai faru, wanda Manzon Allah (s.a.w.a) yana gargadin al'umma ne a kan wannan wulakantarwar kuma yana bayyana tsananin azabar da za ta biyo bayan aikata hakan, ta yadda Allah Ta'ala da kansa zai zama shi ne wanda zai nemi wannan hakkin, wato zai yi hukunci da adalci.
Kuma madamar wadannan ukun su ne asasi na kafuwa da karfafuwar al’ummar musulmi, to wulakanta su yana nufin zagwanyewar wannan al’umma da shafewarta, a saboda haka ya zama dole a gare mu mu dauke su daya bayan daya mu yi bahasi na musamman a kan kowanensu, da kuma salon gudanarwarsa da ya yi amfani da shi wajen inganta rayuwar al’ummar musulmi da yin bayanin tasirinsa da muhimmancinsa a rayuwar ita al’ummar, tare da fayyace tsabagen asarar da za ta yi a yayin da ta juya masu baya.
Kuma ina ganin yana daga cikin abin da ya wajaba a gare ni in danganta kaina (a matsayin mai kira na gama-gari) kamar yadda suke ambato a yau domin in daga wannan korafin guda uku, amma zan fara da yin magana game da mafi nauyi da girma a wajen Allah wato: Qur'ani mai girma wanda yake igiya ce mikakkiya daga gurin Allah Ta'ala zuwa ga bayinsa, wannan koken da korafin wanda Manzon Allah (s.a.w.a) da kansa zai kai a ranar kiyama: “Ya Ubangijina! Lallai jama’ata sun riki wannan Qur’anin abin kauracewa”, Furqan: 30. Kuma ya gargadi musulmi daga wannan hadarin lokacin da ya bijiro masu da sababin karkacewar al’ummun da suka gabata, wanda shi ne barin abin da Allah ya saukar gare su, Allah yana cewa: “Ka ce: Ya ku ma’abota Littafi! Ba ku zama a bakin komai ba, har sai kun tsayar da Attaura da Injila da abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku”. Ma’ida: 8. To duk wanda ya yi riko da shi hakika ya yi riko da hanyar da za ta sadar da shi zuwa ga Allah, wanda kuwa ya juya masa baya to ya halaka ya tabe.
Tushen kai wannan koken da korafin na Qur'ani shi ne juya masa bayan da al'ummarmu ta yi dangane da lamarinsa hatta ma masu wadanda suke masu lizimtarsa[4] daga cikinsu ba su yin tilawarsa ko dan nuna muhimmantarwar gare shi da dan tazakkurin ayoyinsa, to ballantana kuma a ba shi damar ya gudanar da rayuwa da jagorantar lamurran rayuwa domin ya zama wani dalili na shiriyar wasu wadanda za su shiryu da shi a cikin gabaki dayan rayuwa. Don haka sai ya zama abin mantawa a wajensu ba masu tunawa da shi sai ‘yan kadan, su din ma sai a watan Ramadan mai albarka. To mu a nan muna masu kwadaitarwa a kan kara bai wa Qur'ani muhimmanci a cikin wannan watan na Ramadan mai albarka, saboda a samuwar wata alaka ta kud da kud a tsakaninsu. Ya ma zo a hadisi cewa: “Kowane abu yana da dausayi, amma dausayin Qur'ani shi ne watan Ramadan”[5]. Sai dai wannan ba yana nufin sai a shantake a watsar da shi ko kuma a gajarta kulawa da shi a sauran watannin ba.
[1] Al-Kafi, Kitabu fadlul Qur'ani, babin da yake magana a kan karantawa kai tsaye daga shakufan Mus’hafin, hadisi na 3, sai kuma Al-Khisal; juzi’i na 1, shafi na 142, babuka guda uku.
[2] Wasa’ilul Shi’a: Kitabul Salat, babin hukunce-hukuncen masallaci, babi na 5, hadisi na 2.
[3] Wannan ruwayar ta zo a cikin littafan Sunnah da Shi’a, amma ga mai bukatar karin bayani sai ya duba (Al-Muraja’at) na Sayyid Abdul Husain Sharafuddin Musawi.
[4] Na dan zabo wani adadi na daliban na yi bincike a kansu domin neman sani game da alakarsu da Qur'ani sai na gano wasu adadi daga cikin magabata wadanda aka ba su gurbin karatu a Hauzar ilimi ta Najaf, na yi tsammanin darajar saninsu, farkawa da imaninsu ne ya tunkuda su zuwa ga zabar wannan hanyar (maslakin), sai na samu wani bai ma ko yi saukar Qur'anin ba ko da sau daya – amma har ya samu damar hawan mimbari – wani kuma gabaki dayan rayuwarsa sau biyu ya yi saukar, amm da yawa daga cikinsu su suna karanta shi a warwatse a cikin munasabobi na addini. Wannan kawai karatun ne, amma fahimtar ma’anarsa da yin tafakkuri a cikinsa da abubuwan da ya kunsa, sai ka samu a nan hakikan jahilcinsu yake.
[5] Ma’anir Al-Akhbar: shaikh Saduk, shafi 228.