BUDEWA
21/07/2020 18:50:00 |
29/ZULKI’IDA/1441|times read : 387
BUDEWA
Mutane sun saba a yayin bude tarurruka, mu’utamarori, ganawa, shirye-shiryen gidan radio da na gidan talabishin da karatun wasu ayoyi na littafin Allah Qur’ani domin neman albarkarsu da kuma girmama su, hakan ya ci gaba da gudana ga al’ummar musulmi wanda wannan yake nuna haibar Qur'anin har a cikin zukatan makiyansa. To mai zai hana mu daliban Hauza mu bude darussanmu da karatun Qur'ani mai girma, kuma lallai ya kamata budewar ta zama budewa mai cike da farkawa, mai ma’ana wacce ta dace da ruhin Qur'ani, abubuwan da ya kunsa da ma’anoninsa, kada ya zama ana budewa da karatun ne kawai domin kawatawa, jin dadin sautinsa, iya rera karatunsa ko kuma mujarradin rukiyya.