Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

| |times read : 432
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Kuma (ka tuna) a ranar da sama take tsattsagewa tare da gizagizai, kuma a saukar da mala’iku saukarwa. Mulki na gaskia kuma na hakika a wannan rana yana ga mai Rahama, kuma zai zama yini ne mai tsanani a kan kafirai. Kuma a ranar da azzalumi zai ciji hannayensa (saboda dimbin asarar da ya yi) yana mai cewa ya kaicona! Ina ma dai a ce na riki hanyar da Manzo ya rika. Ya kaicona! Ina ma dai a ce ban riki wane (fulan) a matsayin masoyi ba. Lallai, tabbas ya batar da ni daga ambato, bayan ambaton (Qur’anin) ya zo mani, kuma shaidan ya kasance mai kware wa mutum baya ne. Kuma Manzo ya ce: Ya Ubangijina! Lallai jama’ata sun riki wannan Qur’anin abin kauracewa. Kuma kamar haka ne muka sanya makiyi daga mujrimai ga kowane Annabi, kuma Ubangijinka ya isa ga zama mai shiryarwa mai taimako. Kuma wadanda suka kafirta suka ce: Don mai ba a saukar da Qur’ani jimla guda a gare shi ba, kamar haka ne, domin (muna son) mu karfafi zuciyarka game da shi, kuma mun jeranta karanta shi sannu a hankali jerantawa. Kuma ba za su zo maka da wani misali ba, face mun je maka da gaskia da mafi kyau daga fassara.

Al-Furkan: 25-33.