Nauyin Da Ya Hau Kanmu Game Da Bunkasa Musulunci Da Yunkurin Imam Husain (as)

| |times read : 96
Nauyin Da Ya Hau Kanmu Game Da Bunkasa Musulunci Da Yunkurin Imam Husain (as)
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Da Sunansa Madaukaki

Nauyin Da Ya Hau Kanmu Game Da Bunkasa Musulunci Da Yunkurin Imam Husain (as)

Kyautar Imam Husain (as) ba ta kebanta ga shi’a ko musulmai kawai ba, a’a shi wani mai taimako ne wanda gabaki dayan mutane suke kwararowa zuwa gare shi, kuma wannan ba wai cika baki ba ne ba, a’a shi ne ainahin hakikar da shugabanni, malamai, masana da marubuta daga harsuna daban-daban na al’ummu mabambanta suka shaida, haka nan zantukansu da maganganunsu dangane da hakan sanannu ne kuma mashhurai ne.

Wannan hakikar wacce muke rike da ita mu mabiyan Imam Husain (as) kuma har muka san wani abu na zantukan Imam Husain (as) da suke cike da balaga, to ya hau kanmu cewa mu isar da wannan sakon mai albarka zuwa ga sauran al’ummu da kabilunsu da harsunansu masu tarin yawa (a fadin duniya), sannan idan har muka noke ba mu yi wannan ba to mu sani lallai wadannan al’ummun shin mutanen tsaunukan Afrika ne ko kuma na dazukan Amazon ne ko na yammacin duniya da gabacinta ne to za mu tsaya da su a gaba ga Allah Ta’ala muna masu fuskantar tuhuma da tambaya a ranar kiyama suna masu nema a wajen Ubangiji cewa: “Ya Ubangijin Izza da Jalala ka karbar mana hakkinmu daga gurin wadannan mutanen wadanda suka haramta mana sanin albarkokin da ke tattare da Imam Husain (as) ba su isar da sakonsa zuwa gare mu da harshen da muke fahimta ba ta yadda za mu samu mu amfana har mu kwararo zuwa ga albarkokinsa nan nasa ba.

Shin ashe wannan ba daga siffofin Imam Husain (as) ba ne, cewa shi (Fitilar shiriya kuma jirgin tsira ne) ba, a saboda haka wajibi ne haskensa ya riski duk wanda ke neman shiriya, kamala da daukaka don ya hau cikin jirginsa, duk wanda yake son tsira daga nutsewa cikin zunubbai, fitintinu, bata, kaucewa turbar kwarai da fasadi, to wajibi ne ya zama ba a haramta masa da sauran kowa da kowa samun wannan falalar mai girma ba.

Watakila wadannan al’ummun su ce mu kam mun kasance muna ganinku kuna kuka da dukan jikunnanku kuma kuna yin tarurruka na bakin ciki da yin kasidu, amma ba mu iya fahimtar sirrin da ke cikin wannan tashin hankalin (da ku ke ciki), radadin, kukan, ciwon da kuma wannan tururuwar ta miliyoyi a wani yanki na duniya ba duk da girman tashin hankalin da kuma girman wanda ake yi dominsa, ga shi kuma ku ba ku yi mana bayanin falsafar da take cikinsa da yaren da ya dace da al’adunmu da zamantakewarmu ba, sannan ba ku iya gamsar da su ruwayoyin da suke magana kan ladar kuka ko yunkurin kuka ga Imam Husain (as) ba, tun da yake su ba su yi imani da tushen addini ba, amma da a ce mun zo masu ta kofa kuma da harshen da suke fahimta da tausasawar zantuka, muka kuma yi masu sharhi a kan tasirin haduwa, kumaji, halayen kwarai da siyasa har zuwa ga ingancin yin kuka ga Imam Husain (as), to da sun kwankwandi dadin da albarkar yin kukan, wadancan tasirorin wadanda dawagitai da azzalumai suka riska don haka suka hana tarukan tunawa da Ashura suka kuma tinkari lamarin iya karfinsu suna azabtarwa har da wuta da karfe, wanda kafin wannan tun a tarihin baya sun hana Sayyida Fatima Azzahra (as) yin kuka a kan babanta wanda hakan ya tilasta wa Amirul Muminina (as) gina mata gidan bakin ciki domin ta yi kukan rashin babanta (s.a.w.a) a cikinsa.

 To yayin da malami zai haye kan mimbari a kasashen Turai ya dinga bayani a kan musabbabin fitar Imam Husain (as) a kan Yazid cewa ya kasance mai shan giya ne shi, yana buga ganganun kida, yana aikata alfasha, yana wasa da birai da sauran makamantan wannan, to su fa ba lallai ne su ga wannan a matsayin wani abu ba, za ma su iya ganin cewa ai ‘yancinsa ne wannan, koda sun sallama cewa akwai kuskure a cikin wadansu abubuwan, amma dai za su ga ai wannan bai kai a yi fito na fito da mai mulki ba ballantana har a bayar da rai ran ma har da na jariri mai shan nono har kuma aka tasa keyar mafiya karamcin halittar Allah a matsayin ribatattun yaki zuwa fadar mafi wulakantar halittar Allah Ta’ala (Yazid bn Mu’awiya).

Sai dai da a ce za mu sanya zantukan Imam Husain (as) a cikin sabon salon wa’azi wanda zai dace da wannan zamanin na yau mu ce Yazid sace dukiyar ‘yan kasa ya dinga yi ya kuma haramta masu hakkokinsu na shari’a (ya handame su shi kadai), haka nan kuma ya dakatar da aiki da kundin tsarrin mulkin da al’umma suka aminta da shi (ya kashe sunnah ya raya bidi’a, ya haramta abin da Allah ya halasta, ya kuma halasta abin da Allah ya haramta) ya wulakanta alfarmar Qur’ani da sunnah wadanda su ne tsarin mulkin musulmai.

Haka nan kuma ya rugurguza hakkokin dan adam (domin yakan jefa mutum a cikin kurkuku saboda kurum ana zaton ya yi laifi, yakan kuma kashe mutum don kawai ana tuhumarsa da wani laifi) kuma shi ya kasance sarki ne azzalumi kuma ja’iri, ya hau kan karagar mulki ta hanyar kwace da danniya ba a kan son ran mutane ba da dai makamantan irin wadannan, to kuma tabbas wadannan abubuwan sun isa su sanya a yi juyi da yin yunkuri wajen fuskantar azzalumin maketacin shugaba.

Don haka yunkurin Imam Husain (as) ba wai wani motsi ne da zai zama abin da za mu dinga alfahari da shi ga sauran jama’a ba, mu kuma dinga tunanin cewa mun bayar da wani abu ga Imam Husain (as) ko mu dinga jin mun yabe shi irin yadda ya cancanta a ce an yabe shi din, a’a wannan wani babban nauyi ne da ya hau kawukanmu a matsayinmu na masoyansa masu biyayya gare shi (as) mu tsaya tsayin daka wajen ganin mun yi magana da dukkan al’ummomi bisa al’adunsu da harsunan da suke fahimta, da kuma fahimtar yanayin da suke rayuwa a ciki da dukkan jama’arsu har da masu zowa nan gaba gwargwadon iko, ta yadda kowa zai sami Imam Husain (as) a matakin rayuwa a matsayin wanda ya wadatar kuma abin koyi, wanda a irin haka ne ma aka samu cewa an ce Imam Husain (as) shi ne mafi girman jirgin tsira.

Wannan nauyi ne da yake nema daga gare mu cewa mu yalwata kayan aikinmu mu kuma rungumi dukkan kwazo da himma domin samun nasara a wannan aikin. 

Sannan duk wata gazawa a cikin gudanar da wannan aikin to mu ababen tambaya ne a kansu, wanda mafi tsananin tambayar ita ce idan ya zama mu ne da kanmu muka gurbata wannan ibadar, sai ka ga an nisantata ta hanyar zantuttuka daban-daban tare da sanya shingaye da shamaki a cikin imanin mutane game da al’amarin Imam Husain (as) ko kuma a yi amfani da hakan wajen gurbata Musulunci da mazhabar shi’a kamar yadda ayyukan wasu masu mulki da sunan addini da mazhaba suke jawowa, abin da yake sabbaba wasu su tsani addini, to a irin wannan lokacin hisabin zai kasance mafi tsanani kuma zai zama abin rubanyawa, sannan al’umma za ta tuhume mu a kan mun haramta mata samun albarkokin da ke tattare da wannan ni’ima mai girma.

Shin da yawa daga cikin ‘ya’yanmu ba suna kammala karatunsu na digiri a kwalejojin harsuna suna karantar harsuna daban-daban na duniya duk shekara ba, kuma suna lakantar harsunan har suna yin magana da su kawai dai matsalar ba su samun damar aiki ne ba, ko kuma a’a suna samun aikin sai dai ba wanda suke da kwarewa a kansa ba ne, to mai zai hana mu mu samar masu na’urorin zamani wadanda za su dinga aiki da su, suna tabligin isar da sakon Musulunci mai tsarki na asali zuwa ga sauran al’ummu ta hanyar harsuna daban-daban.

Don haka abin da muke bukata ba wai mu zamanantar da salon wa’azin Musulunci ba ne da yunkurin Husain (as) kawai ne ba, a’a kari a kan haka har da irin sabon salon isar da sako ta hanyar amfani da sauran harsunan zamani da kayayyakin aikinsa da yadda zai isa ko ina da ina na jama’ar da ke zaune a doron kasa da sauran masu zo wa nan gaba ma.

To sai dai kafin aiwatar da hakan, wajibi ne a gare mu mu shirya kawukanmu a aikace da tunani da dabi’u na gari.

Abu Salt Al-Harawi ya ruwaito cewa: “Na ji baban Hasan Ali bn Musa Al-Ridha (as) yana cewa: Allah ka ji kan bawan da ya raya al’amarinmu. Sai na ce masa kamar yaya zai raya al’amarinku. Sai ya ce: Zai koyi ilimominmu sannan ya koyar da su ga mutane, domin idan mutane suka san kyawawan zantukanmu, hakika za su bi mu”, (Uyunu Akhbarir Ridha; 1/275 a cikin babi na 28, hadisi na 69, da kuma Ma’anil Akhbar; 180.

A cikin wannan hadisin akwai nukudodi masu yawa:

1-    Cewa a cikin raya al’amarinsu (as) yana zama sanadin samun rahamar Allah wanda muke dokin samu, sai dai hakan kawai ba ya wadatarwa mu bayyanar da tarurruka na zahiri domin wadannan a matsayin wasila ce kawai ta isa ga hakikanin sakonsu (amincin Allah ya tabbata a gare su), (to sannan sai ya koyar da su ga mutane).

2-    Dole kafin koyar da mutanen, ya zama an yi zurfi cikin sanin ilimominsu, kyawawan halayensu da sanin tarihin yadda suka gudanar da rayuwarsu da zantukansu masu albarka.

3-    Kuma lallai ita natija (wacce ita ce bin Ahlul Baiti (as)) tabbas za ta hakkaku ne ta hanyar isar da zantukansu kamar yadda suke a kyawonsu, kyalkyalinsu da haskakawarsu da mutuntakarsu, kuma mu abin da ya hau kanmu shi ne sadar da kyawawan zantukansu (amincin Allah ya tabbata a gare su) zuwa ga mutane ba tare da mun yi kari ko ragi daga wajenmu ba da tunanin cewa hakan shi ne kyautatawa.

4-    Cewa sakonsu na duk duniya ne ga kowa da kowa baki daya, don haka ba ya kebanta ga shi’a kawai ko musulmai kawai ba a’a, kamar dai yadda yake a sakon kakansu Al-Mustafa (s.a.w.a). Allah ya ce: “Kuma ba mu aiko ka ba face domin wata rahama ga talikai”, (Anbiya’i, aya ta 107). Da kuma: “Domin ya kasance mai gargadi ga halitta (gabaki dayanta)” (Furkan, aya ta 1). Wannan kuma shi ne abin da muke yin ikirari da shi yayin ziyararmu ga Imam Husain (as) da kuma yin bayani na hadafin yunkurinsa mai albarka, “Kuma ya bayar da ransa da jininsa a kan hanyarka (ya Ubangiji) domin ya ‘yanto bayinka daga duhun jahilci da sauka a kan mikakkiyar hanya ta shiriya”. (Mafatihul Jinan; 773 Ziyarar Arba’in).