Ayatullah Yakubi A Ganawarsa Da Ba-Faranse Masanin Gabas (Mustashrik) Ya Ce: Lallai Addinin Musulunci Shi Ne Tushen Ci Gaba Da Wayewar Kasashen Larabawa Kuma Shi Ne Mai Jagorantar Ci Gaban Bil Adama A Tsawon Tarihi.

| |times read : 13
Ayatullah Yakubi A Ganawarsa Da Ba-Faranse Masanin Gabas (Mustashrik) Ya Ce: Lallai Addinin Musulunci Shi Ne Tushen Ci Gaba Da Wayewar Kasashen Larabawa Kuma Shi Ne Mai Jagorantar Ci Gaban Bil Adama A Tsawon Tarihi.
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Ayatullah Yakubi A Ganawarsa Da Ba-Faranse Masanin Gabas (Mustashrik) Ya Ce: Lallai Addinin Musulunci Shi Ne Tushen Ci Gaba Da Wayewar Kasashen Larabawa Kuma Shi Ne Mai Jagorantar Ci Gaban Bil Adama A Tsawon Tarihi.

Ranar Laraba daya ga Sha’aban 1439

Daidai da 18/4/2018

Marji’in addini samahatul shaikh Yakubi (Allah ya tsawaita kwanansa) ya karbi bakuncin Ba-faranse mai bincike Farfesa Gilles Kepel[1], kwararre kan al’amuran zamantakewar musulmi kuma mai yakar tsattsauran ra’ayi malami a kwalejin Nazarin siyasa a Paris, tare da rakiyar wasu abokan tafiyarsa a ofishinsa da ke Najaf mai tsarki.

Bakon ya yi burin ya zama daya daga cikin muhimman abubuwan da zai gudanar a ziyararsa ta farko a birnin Najaf mai tsarki ita ce ganawa da maraji’ai, domin yana da fata a kan cewa lallai zai samu irshadodi da jin ra’ayoyinsu game da makomar yankin wanda a ‘yan shekarun baya-bayan nan yake fuskantar hujumin ‘yan takfiriyya da masu fandarewa, (kuma abin takaici) bisa zalunci sun dauki addinin Musulunci a matsayin abin da suke fakewa da shi wajen yin munanan ayyukansu, haka nan kuma bakon yana matukar son ya san wane mataki ne Maraji’ai suke dauka domin sake gina daular Iraki.

A cikin jawabinsa ya tabo wasu bagarori na tushen fikirar da akidar da mazahabar Ahlul Bait (as) take tarkizi a kansu wadanda kuma wani bangare ne da ya shafi yanayin tambayoyin Farfesa Gilles wadanda ya yi masa, samahatul shaikh Yakubi (Allah ya tsawaita kwanansa) ya bayyana masa cewa lallai koyarwar shi’anci ta ginu ne a kan girmama bil adama kai hatta sauran halittun da ba mutane ba ma, don ya zo a hadisin Kudusi cewa: “Ababen halitta zuriyata ne, kuma mafi soyuwarsu a wajena shi ne wanda ya fi tausasawa ga ababen da na halitta”. Wannan kalmar ta ‘ababen halitta’ a nan tana nufin duk gabaki dayan halitta ba wai ta takaitu a kan dan adam ne kawai ba…. kamar kuma yadda ya zo a wani hadisin Kudusin cewa: “Mumini ya fi Ka’aba girman daraja da kima”… Don haka Musulunci a bisa fahimtar makarantar Ahlul Bait (as) ya ginu ne a kan girmama kowa da kowa da kuma yada al’adar kawo daidaito da rangwantawa da aminci… kai fiye da haka ma wato ya koyar da yin mu’amala cikin kauna da son juna, an samu hadisi daga Imam Sadik (as): “Shin akwai wani abu da ake kira addini in ba soyayya ba”[2].

Kamar yadda samahat shaikh ya ankarar a kan cewa shi Musulunci ya muhimmantar da a zauna a tattauna domin a warware wata rashin jituwa koda ko da abokin husuma ne, wanda a sarari za mu ga hakan a cikin tarihin rayuwar Manzon Allah (s.a.w.a) da Imamai Ahlul Baitinsa (as), haka nan za ka ga Amirul Mumina Ali dan Abi Dalib (as) a matsayinsa na khalifa na shari’a kuma wanda al’ummar musulmi suka hadu a kan khalifancinsa ba tare da jayayya ba, yana tsananin kiyaye zubar da jini da kare rayukan mutane wanda sai da ya shekara daya cur yana aikawa Mu’awiya (tare da kekashewarsa da kafewarsa ta kin yin biyayya ga khalifan da shari’a ta amince da shi) wasiku, wa’azi da shiryatarwa kafin ya fara yaki da shi, kuma za ka ga yadda Imam (as) ya aika dan baffansa, sahabin Annabi (s.a.w.a) Abdullah bn Abbas domin ya tattauna da Khawarijawa tare da tunatar da su da yi masu wa’azi sai ga shi ya samu nasarar fadakar da mutum 6000 daga cikin 9000 har suka dawo kan hanyar gaskiya.

Samahatul shaikh bai tsaya a nan ba sai da ya bayar da misali kan abin da ke gudana a halin yanzu cikin lokacin nan namu wato shi a kan kansa yana kira game da yadda za a zauna a magance gurbacewar tunani da addini da kafirta sauran jama’a, ta hanyar tumbuke tushen akidar ta wadannan jama’ar wacce suke riko da ita har ta zamo sanadiyyar ganin halascin ayyukan nasu, a saboda haka ya bude kofa wacce za ta bayar da damar haduwa a zauna a tattauna da fatan a iya isa ga nasara wajen warware lamarin, domin da yawa-yawan masu karkacewar nan suna fama da rudu ne a kwakwalensu wanda ya yi tasiri a cikin tunane-tunanensu, sannan kutsawa cikinsu ba tare da an saita masu tunaninsu ba zai iya zama asara.

A nan samahatul shaikh ya kara maimaita kiransa ga ‘yan uwanmu ahlul Sunnah a kan su bude kofar ijtihadi wanda aka kulle shi a bangarensu tun a zamanin imaman mazhaba, domin a dinga bayar da damar yin ijtihadi ga wadanda suka cancanta kawai, don a toshe kofar fatawoyi barkatai, wanda idan aka yi haka sai ijtihadi ya zama yana da ka’idodin da za a killace shi ga wadanda suka cancanta masu ilimi da kyawawan dabi’u kurum domin (ilimi da kyawawan dabi’u) su ne sharuddan ijtihadi da adala a wajenmu.

Dangane da abin da ya kebanci rawar da marja’iyya za ta taka kuwa samahatul shaikh ya yi jaddada jawo hankalin maraji’ai a kan su muhimmantar da hadin kan ‘yan kasa, su kiyaye maslahohin al’umma da nuna masu hanyar da za ta kai su ga tudun mun tsira, su inganta masu tattalin arziki, su sanya masu son kasarsu, duk da dai mukan sami irin hakan a sarari a tsakankanin ‘yan kasa tare da bambance-bambancen mazhabobinsu da kabilunsu a matakai da kuma munasabobin kasa da kalubalen da kasa take fuskanta ta bangaren tsaro da sauransu.

Samahatul shaikh ya nanata maganarsa a kan cewa lallai ne maraji’an addini su dinga ji a jikinsu cewa akwai nauyi a kansu na wannan kasa da ‘yan kasar, sai dai ka da su tsunduma kansu da yawa cikin halin da sha’anin siyasa ya samu kansa a ciki, domin wannan ba bangare ne da ya hau kansu ba kwata-kwata, sai dai kawai su shigarsu za ta kasance ne a matsayin masu kariya ga maslahohin mutane da rayukansu da kare mutanen Iraki daga sharrin karkatattun akidu kamar shigowar Da’ish cikin kasar da makamantansu… Wannan dai ita ce mahangarsu kan rawar da za su taka cikin wannan halin. 

Samahatul shaikh ya bayyana damuwarsa a kan kokarin da wasu suke yi na raba tsakanin Musulunci da ci gaban zamani, da mayar da shi lamarin da yake da alaka da al’ummar zamani da hukumar zamani suna masu kishiyantar hukumar da take tsamo dokokinta daga hukunce-hukuncen Musulunci, yayin da shaikh ya kara bayyana cewa lallai addinin Musulunci shi ne tushen ci gaba da wayewar kasashen Larabawa kuma shi ne mai jagorantar ci gaban bil adama a tsawon tarihi, don duk wanda ke bibiyar al’amuran Larabawa kafin zuwan musulunci ba abin da zai gani sai wasu tsirarun mutane masu kaiwa junansu hare-hare, amma albarkacin musulunci suka wayi gari masu hukuma wayayyiya wacce ta gadar masu da al’adu kyawawa ta inganta masu tunaninsu. Daga karshe suka zama su ne suke jagorantar duniyar dan adam.

Haka nan kuma ya yi nuni a kan cewa da yawan ka’idojin bil adaman da muke girmamawa a Turai kuma ake tinkaho da su za ka samu tushensu daga Musulunci ne…. musulmai ba su ja baya daga matsayinsu na manyan mutane wayayyu ba sai saboda ko in kula dinsu ga ka’idoji da darajojin addinin Musulunci mai girma, yana mai kara jaddada cewa duk kuwa da cikar tsarin na Musulunci da gamewarsa kan komai da komai…. Domin shi addini ne mai ginawa, kerawa da samar da farin ciki da walwala ga al’umma da garuruwa, kuma addini ne mai kawo ci gaba da wayewa.

A karshen ganawar, bakon ya nuna jinjinawarsa da girmamawarsa ga samahat Ayatullah Yakubi a matsayin mutum mai yalwar kirji sannan ya yi masa godiya game da abubuwan da ya ambata.

Taron ya samu halartar manyan jami’ai na ma’aikatar harkokin kasashen wajen Iraki wadanda su ne suka shirya wa bakon wannan ganawar.  

 

 

 [1] - Farfesa Gilles Kepel babban malamin jami’a kuma shugaban cibiyar Nazari a kan Gabas ta Tsakiya da yankunan Mediterranean a kwalejin nazarin siyasa a Fransa, sannan malami ne mai kulawa da duba rubuce-rubucen daliban ilimi (academic) a kan harshen Larabci da addinin Musulunci a matakan karatun digiri na farko, na biyu da na uku wato dakta, haka nan kuma shi ne wanda ya assasa tashar (Eurogolfe) a 2013, a yanzu kuma shi ne shugaban majalisar gudanarwar tashar, haka nan kuma ya kasance malami (visiting lecturer) mai kai ziyarar koyarwa a jami’ar New York da jami’ar Colombia a wajajen 1995 – 1996. Yana dauke da kwalayen digirin digirgir a kan harshen Larabci, Ingilishi da falsafa, sannan yana da digiri a kan science daga kwalejin koyarwa ta siyasa, kuma ya karbi kwalinsa na dakta a fannin sociology da ilimin siyasa.

[2] - Al-Khisal, 21/73