Kwayar cutar korona (coronavirus) tana caccanja duniya sannan tana sake sabunta shakalinta

| |times read : 13
Kwayar cutar korona (coronavirus) tana caccanja duniya sannan tana sake sabunta shakalinta
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Kwayar cutar korona (coronavirus) tana caccanja duniya sannan tana sake sabunta shakalinta

 

Marji’in Addini Shaikh Yaqubi:  Wa’azi Da Jan Hankali Daga Annobar Corona (coronavirus)

1- Da yawa daga cikin abubuwan da suke afkuwa wadanda suke haifar da tashe-tashen hankula, kuma har ma su kan kasance sanadin fadawar wasu cikin kuncin rayuwa a daidaikunsu da a jama’arsu zai yiwu su zama wadansu abubuwa ne masu kyau da amfani idan da za a yi masu wani kallon ta wata fuskar daban, kuma za ka samu ainahin wannan ma’anar a cikin fadin Allah Ta'ala: “Yana da wani kyaure, a cikinsa nan rahama take, amma a bayansa daga bangaren wajensa azaba ce”[1] Hadid: 13.

2- Lallai yi wa al’amuran kallo mai kyau yana taimakawa wajen tabbatatuwa da karfafuwar rai da natsuwar zuciya da kuma yarda a kan abin da yake gudana, sannan yana kubutarwa daga dukkan firgici da tsoro wanda hakan yake gurguntar da rayuwa da jawo yanke tsammani da rushewa, da tunkuda mutum zuwa ga bijirewa da rashin bin ka’idodin kiwon lafiya kamar yadda (a mahangar kwararru) sun nuna cewa hakan yana jawo raunin garkuwar jiki da yiwuwar fadawa cikin lalurar kamuwa da rashin lafiya.    

3- Shi irin wannan kallon wato a kalli annobar ta janibin kyawonta zai yiwu ainahin ita wannan annobar ta corona a canza salon kallonta maimakon kallon da ake yi mata a matsayin cuta sai a kalle ta a matsayin sanadi ta warakar abubuwa da yawa daga cikin cututtukan rai, zamantakewar al'umma, siyasa da cutar fikira. Duba ka ga irin yadda wannan cutar nan (coronavirus) ta haifar da wani irin tsoro da tsananin firgici da gazawa kawai domin ta fitar da mutane daga halin gafala da sabon Allah Ta'ala zuwa ga halin biyayya da sallama wa kudurarsa marar iyaka da dawo da su cikin hayyacinsu domin su koma ga Allah Ta'ala shi kadai tare da yin magiya a gare shi saboda ya yaye masu wannan bala’in[2].

4- Wannan cuta (coronavirus) tana bayyanar da hakikanin wannan ayar mai girma a fili: “Misalin wadanda suka riki wadansu masoya wadanda ba Allah ba kamar misalin gizogizo ne wanda ya riki dan gida, alhali kuwa mafi raunin gidaje shi ne gidan gizogizo” Ankabut: 41.

      Lallai babu ko shakka cewa gazawar karfin Fir’aunoni masu ganin cewa su ne masu iko a kan dukkan komai babu wani abu da ya isa ya fita daga saidararsu ta bayyana a sarari, sai ga sojojinsu na kasa da na ruwa, da fasaharsu wacce suka tanade ta domin yakar rundunar da ke a sararin samaniya ballantana kuma rundunar kasa, amma tattare da haka sun gaza gurin iya aikata wani abu game da yaduwar wannan annoba. Kuma sai annobar ta juyar da akalar dukiyoyi masu dimbin yawa wadanda suke batarwa wajen tara makaman yaki a cikin rumbuna domin kiyayyarsu ga al'umma zuwa ga yin hidima ga bangaren lafiya da taimakom jama’a, kamar yadda ta dakatar da tarurrukansu wadanda suka kasance suna aiwatarwa domin kirkiro munanan tsare-tsarensu na zaluntar al'umma da kwace masu arzikinsu.   

5- Lallai wannan ibtila’in na wannan annobar (coronavirus) wani fage ne na gano dabi’ar al'ummar kasa da abin da suka ginu a kai na mabambanta tunaninnikansu na yadda tasowarsu ta kasance da irin kyawawan halayensu, domin za ka ga yayin da wasu mutane masu yawa suka bazama wajen shiga cikin ayyukan agaji a cikin kasashenmu domin bayar da tallafi wajen ganin an shawo kan da magance wadanda suka kamu da cutar da kuma bizne wadanda suka rasu cikin girmamawa da karramawa, tare da taimakon iyalai wadanda hanyoyin neman arzikinsu suka tsaya cik saboda wannan halin da aka shiga ciki na rashin kai-komo, zaman gida da kebance masu fama da cutar wuri guda, da kuma tallafawa da kunshin kayan abinci kyauta a gare su, da tsaftace tare da yin feshi a gidajen wanka da bahaya na jama’a da unguwanni, a daidai lokacin ne kuma za mu samu wasu daga cikin hukumomin kasashen yamma suna kira ga aiwatar da siyasar (herd immunity) wacce take nufin rashin daukar matakin bayar da rigakafin da ya dace domin kare al'ummar kasa da sakacin barin annobar ta fantsama cikin jama’a tana kama na kamawa mai rabon tsira ya tsira a sakamakon garkuwar da jikinsa take dauke da ita, tsofaffi kuma su mutu da wadanda suke cikin lalaurar fama da wasu tsofaffin cututtuka a jikunnansu ba tare da an samar da yalwatattun kayan aiki da kulawa ta musamman gare su ba, har dai annobar ta gushe wasu su tsallake su tsira wadanda kuma ba su samu kulawa da samun kariya daga cutar ba mutuwa ta riske su. Duk da cewa hukuma tana karbar haraji daga dukkanin ‘yan kasa a tsawon lokacin ayyukansu wanda a irin hangensu da tsarinsu dama ana tanadar irin wadannan kudaden ne domin yin hidima ga al'ummar kasa baki daya, amma ba tare da bayar da wannan tallafin na jama’a gare su ba.  

Kuma da haka ne karama da mutuncin dan’adam suak fadi kasa warwas a wurinsu musamman tsofaffi wadanda mu a cikin shari'armu (ta musulunci) suna da hakkin a ba su kowace irin kulawa da girmamawa.

6- Lallai dukkan abin da yake gudana da wanda zai gudana a nan gaba yana yin hannunka mai sanda ne ga bil’adama da su koma su binciki tunaninnikansu, yadda suke gudanar da rayuwarsu, tafiyar da halayensu da abubuwan da suke fifitawa wadanda suka yi amanna da su. Kuma ya kamata kwararrun masanansu da malaman falsafarsu su dage wajen ganin sun kawo wani motsi na samun canji wanda zai game dukkan wadanda suka samu tajruba ta wannan annobar coronavirus din da abin da ya haifar da ita da masu raunanata tun kafin lokaci ya kure domin ba mu cikin aminci daga wannan ibtila’in daga wani lamarin daban wanda aka gaza fuskantarsa koda ‘yan wasu hanyoyi wadanda aka ci nasara da su wajen killace corona daidai wani gwargwado.

7- Lallai ibtila’in nan na wannan annobar daya ne daga cikin da yawa daga sakamkon munanan ayyukan dan’adam wanda shi da kansa ya janyo su ga kansa da kuma ga sauran al'umma gaba daya, saboda rashin kiyayewarsa “Kuma abin da ya same ku na wata musiba, to daga abin da hannayenku ne suka sana’anta, kuma Allah yana yafe masu yawa”[3] Shura: 30, kuma yana tunkude wa halittunsa da yawa daga wadannan bala’oin “(Kowanne dayanku) Yana da wadansu mala’iku masu maye wa juna a gaba gare shi da a baya gare shi, suna tsare shi da umarnin Allah” Ra’ad: 11, “Lallai Ubangijina mai jin kai ne, mai nuna soyayya (ga bayinsa)” Hud: 90.

8- Wannan ita ce alakar soyayya wacce ta ginu a kan rahama da jin kan Allah tsakaninsa da bayinsa, duk da dai cewa ta kasance daga bangare daya ne kawai domin shi mutum ba ya kaddara wannan soyayyar kuma ba ya ba ta hakkinta kamar yadda ya kamata[4] “Kuma ba su kaddara Allah hakikanin kaddarawa gare shi” An’am: 91, sai dai Allah yakan ga a sakamakon wata maslaha ga bawan nasa sai ya kyale shi da kansa, da kuma abin da hannayensa suka shuka ba tare da ya tunkude masa ba, kuma mala’ikun nan masu ba shi kariya su ma sai su kawar da hanayensu daga ba shi kariyar da suke yi bayan sabawarsa da zunubbansa sun yawaita na tsawon lokaci yana yi ba kakkautawa sai ya wayi gari mai cutarwa ga kansa da sauran mutane. Sai a bar shi ya yi fama da mummuan sakamakon ayyukansa duk domin maslaharsa tare da fatan ko ya dawo ga shiriyarsa ya gyara abin da ya bata na daga al’amarinsa[5].

9- Ya wajaba a kan muminai su wa’aztu bisa la'akari da hanawar da aka yi masu ta kai ziyara a Dakin Allah (Haramin Makka) da Masallacin Annabi masu alfarma da haramomi masu daraja na Ma’asumai (as), da kuma dakatar da sallolin jam’i a masallatai, zikirori da ambaton Allah da addu’a a cikinsu, kuma su guji kada su zama su ne abin nufi a cikin fadin Allah Ta'ala: “Kuma idan kuka juya baya (daga yi masa da’a) zai musanya wadansu mutane wadansunku sannan ba za su kasance kwatankwacinku ba” Muhammad: 38.

Muhammad Al-Yaqubi – Najaf Mai Tsarki.

28 Rajab 1441 AH

23 – 3 – 2020 AD[1] Duba Tafsirin ayar a cikin Mausu’atu Kidabul Marhala, Juzu’i na 8 shafi na 164 – A cikin Tafsirin (Min Nuril Qur'ani) juzu’i na 1, shafi na 272 a karkashin unwanin: Wa’azi daga surar Hadid.

[2] Wasu daulolin yammacin Turai wadanda suka kasance suna hana kiran sallah a bayyane kamar Italiya da Spain da Jamus sun bayar da damar a kira sallar a  bayyane ta hanyar amfani da lasifiku domin samar da natsuwa da sakankancewa ga al'ummar kasa. Kuma shugaban kasar Amurka Trumph ya shelanta a ranar 15 – 3 – 2020 a matsayin ranar al'ummar kasa domin yin addu’a. Kuma wasu masu rahoto sun nakalto a ranar 19 – 3 – 2020 daga bakin Firayim ministan Italiya Guiseppe Conte fadinsa: “Lallai mun rasa ikonmu a kan wannan annobar, tana ta kashe mu rayukanmu da jukunnanmu da hankullanmu, babu abin da za mu iya, lallai gabaki dayan wasu damarmakin warware wannan lamari sun kare a kan doron wannan kasar, damar warware wannan matsalar a sama kawai tayi saura”. Tare da sanin cewa lallai Italiya tana daga cikin mafiya cutuwa dangane da wannan annobar ta bangaren masu mutuwa, kuma lallai wasu daga cikin masu aiko da rahotanni sun ji a jikinsu bayan wasu kwanaki da yada labarin sai suka hana ci gaba da yada wannan bayanin  wanda Conte ya gabatar  a dokance, kuma wai Italiya ba ta shelanta sallamawarta ga wannan annobar ba, wata kila hakan ya faru ne ba bisa gamsuwar ba, kuma duk da a cikin zantukansa babu  abin da zai janyo wata damuwa amma suka nace a kan kore shi kawai saboda kasancewarsa mai farfado da janibin addini.   

[3] Duba Mausu’atu Khidabil Marhala: Khidabul Marhala, mujalladi na 11, shafi na 201 – da cikin Tafsirin (Min Nuril Qur'an):  mujalladi na 4, shafi na 272, a wajen bayanin wannan ayar mai girma.    

[4] Duba Mausu’atu Khidabil Marhala: Khidabul Marhala, mujalladi na 9, shafi na 472  – da cikin Tafsirin (Min Nuril Qur'an):  mujalladi na 1, shafi na 224, a cikin tafsirin fadin Allah Ta'ala:  “Kuma ba su kaddara Allah hakikanin kaddarawa gare shi” Hajj: 74,

[5] Duba Mausu’atu Khidabil Marhala: Khidabul Marhala, mujalladi na 9, shafi na 171 – da a cikin Tafsirin (Min Nuril Qur'an): mujalladi na 1, shafi na 85, a wajen yin sharhin wannan fikirar a karkashin fadinsa Ta'ala: “(Kowanne dayanku) Yana da wadansu mala’iku masu maye wa juna a gaba gare shi da a baya gare shi)” ayar da aka ambata a baya.