Hudubobin Babbar Sallar Ta Shekara Ta 1439 AH

| |times read : 13
Hudubobin Babbar Sallar Ta Shekara Ta 1439 AH
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Hudubobin Babbar Sallar Ta Shekara Ta 1439 AH

Da Sunansa Madaukaki

Ranar Laraba 10 Ga Zulhijja Mai Alfarma 1439 AH

Samahat marji’in addini mai girma ayatullah shaikh Muhammad Yakubi (Allah ya tsawaita kwanansa) ya jagoranci cincirindon muminai limancin babbar sallah mai tarin albarka a birnin Najaf mai tsarki.

Sannan ayatullah din ya gabatar da hudubobin sallar yana mai tsayuwa a gaba ga wadannan muminai.

A huduba ta farko, a cikin fadin Allah Ta'ala: “Kuma mutum ya kasance mai gaggawa ne”, (suratul Isra’i aya ta 11). Ku sani a cikin gaggawa akwai nadama sai dai idan an yi ta ne a cikin aikata alheri.

Amma a cikin hudubarsa ta biyu ya yi bayani ne a kan (darasin da ke cikin ruwayar nan ta littafin Sajjadiyya).

A cikin hudubar samahat marji’in addini (Allah ya tsawaita kwanansa) ta farkon nan dai ya yi duba ne a kan wasu daga cikin halayen mutane da abubuwan da suke dauke masu hankali na sha’awace sha’awace wadanda Qur’ani mai girma ya yi bayaninsu, Allah yana cewa: “Lallai mutum an halicce shi mai tsananin kwadayi”, (suratul Ma’arij aya ta 19). Mutum ma’abocin zalunci da jahilci ne, kamar inda Allah ke fada: “Sai shi mutum ya dauketa, lallai ne shi ya kasance mai yawan zalunci, mai yawan jahilci”, (suratul Ahzab aya ta 72), da dai sauran halaye.

Sannan samahatul shaikh ya yi ishara a kan cewa wadannan halayen ba ana nufin halaye ne da aka halicci mutum da su a zatinsa, hakikarsa da asalin halittarsa ba a’a, shi mutum an halicce shi ne a bisa fidirarsa domin ya zama mafi kyawon tsayuwa da daidato kamar dai yadda ya zo a Qur'ani cewa: “Lallai ne mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa da daidaito”, (suratul Tin aya ta 4).

Sai dai abin da wadancan halayen suke nufi shi ne cewa wadansu halaye ne wadanda mutum yake aikata su a doron kasa wadanda suka sabawa ainahin halitta da fidirarsa sakamakon rashin kulawa da kiyaye abubuwan da Allah Ta’ala ya so shi da aikatawa, a sabanin haka sai ya biyewa son ransa sai duniya ta rude shi, sai shaidan ya kawata masa ayyukansa.

Sannan samahatul shaikh a cikin hudubarsa ta farko ya fi mayar da hankali ne a kan daya daga cikin halaye da sha’awace sha’awacen da mutum ya fi karkata gare su wato gaggawa da rashin bi sannu a hankali a yayin daukar matsaya da yanke hukunci sai kawai mutum ya yanke hukunci cikin rashin sani daga nan kuma sai ya jefa kansa cikin bala’i, Allah ya ce: “An halitta mutum daga gaggawa, da sannu zan nuna maku ayoyina, saboda haka kada ku nemi yin gaggawa”, (suratul Anbiya’i aya ta 37).

Sannan samahatul shaikh (Allah ya tsawaita kwanansa) ya ci gaba da yin bayanansa game da wannan yana mai cewa (a saboda haka ya hau kan mutum ya zama mai hakuri kuma mai bi sannu a hankali domin ya isa ga bukatunsa da sha’awarsa kuma ya tabbatar abin da zai yin ya dace da shari’a kuma abu ne mai tsarki mai kiyaye mutunci, an ruwaito daga Annabi (s.a.w.a) cewa: “Lallai abar da ta halaka mutane ita ce gaggawa, kuma da a ce mutane za su sanya natsuwa to da ba za a samu wanda zai halaka daga cikinsu ba”.

Sannan sai samahatul shaikh ya ba da misali a kan gaggawar dan adam wacce take abar zargi inda ya ce: Duk wanda yake son arzikinsa ya yawaita to ya koyi ha’inci, sata, danne dukiyoyin mutane da sauransu na daga cikin hanyoyin da suka sabawa shari’a, misali na biyu kuma shi ne na matashi da matashiya wadanda suka zaku su samar da alaka a tsakaninsu wacce ta sabawa shari’a, shin shari’ar nan ta addini ce ko ta zamantakewar jama’a, a yayin da za ka ga budurwar ta fada cikin tarkon saurayin nan sai ya yaudare ta sannan ya gudu ya barta cikin wahala, haka nan kuma a kan samu wasu ma’aikata masu hana kulluwar wata mu’amala ta jama’a domin sukan tursasa su sai sun ba su cin hanci, amma da sun bari mu’amalar ta gudana cikin sauki da annashuwa akwai yiwuwar mutumin ya yi masu alheri a bisa radin kashin kansa a cikin fara’a da walwala wacce za ta nisanta su daga cin haramun din da suke ta yi wa gaggawa.

 

 

Da Sunansa Madaukaki

A cikin hudubarsa ta biyu samahat marji’in addini ayatullah shaikh Muhammad Yakubi (Allah ya tsawaita kwanansa) ya yi magana ne a kan hadisin da ya zo ta hanyar Imam Zainul Abidin (as) wanda farkonsa ya fara da: “Ya Allah ka ba ni ikon kauracewa wannan gida (na duniya) mai rudarwa, ka ba ni ikon karkata da kuma kwadayin komawa gidan dawwama (Lahira) da yi wa mutuwa tanadi kafin zuwanta”.

Haka nan kuma samahatul shaikh (Allah ya tsawaita kwanansa) ya kara ambato wasu karin hadisai wadanda suke yin magana a kan yi wa mutuwa tanadi…… daga cikinsu akwai wanda aka ruwaito daga Amirul muminina Ali (as) yana cewa: “Lallai ne duk mai hankali ya kamata ya dinga yi wa kansa kashedin cewa mutuwa fa tana nan tafe a wannan gidan na duniya, don haka sai ya kyautata dabi’unsa kafin ya je gurin da zai yi fatar mutuwar amma ina ba zai sameta ba”.

Kamar yadda samahatul shaikh ya yi nuni a kan ayoyin Qur'ani mai girma da suke nuna cewa yi wa mutuwa tanadi da kuma rashin gujewa mutuwar da kinta alama ce ta gaskatawar imani da kaunar Allah Ta'ala, Allah Azza Wa Jallah yana fadin cewa: “Ka ce ya ku Yahudawa idan kun riya cewa ku ne zababbun Allah sabanin sauran mutane, to ku yi burin mutuwa idan kun kasance masu gaskiya”, (suratul Jumu’a aya ta 6).

A cikin jerin bayanansa (Allah ya tsawaita kwanansa) game da yadda ya kamata a yi wa mutuwa tanadi ya kawo ruwayar da wasu littafan kyawawan halaye suka kawo wacce bangarorinta suka zo a cikin ruwayoyi daban-daban, kuma tana a kan matakai daidai gwargwadon irin halin da mutum zai fuskanta a ranar Lahira; wani mutum ya zo wurin Annabi (s.a.w.a) ya ce: “Ina burin in mutu……”.

Bayan kammala hudubobin guda biyu samahatul shaikh ya gana da dandazon muminai da masoya wadanda suka zo sallar idi inda aka taya juna barka da sallah.

Domin ganin kammalalliyar hudubar ana iya shiga wannan link din:

https://youtu.be/Rks5Uzo5OCE