Nasarar Da Ake Samu Ta Hanyar Muzahara (Motsawar) Da Ake Yi Domin Neman ‘Yancin Iraki

| |times read : 573
Nasarar Da Ake Samu Ta Hanyar Muzahara (Motsawar) Da Ake Yi Domin Neman ‘Yancin Iraki
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Da Sunansa Madaukaki

Nasarar Da Ake Samu Ta Hanyar Muzahara (Motsawar) Da Ake Yi Domin Neman ‘Yancin Iraki

Na yi imani cewa daga cikin mafi girman nasarar da wannan motsin na wayayyun tsayayyun dakakkun matasa ya haifar shi ne maido da usuli, tushe da martabar ‘yan kasanci, abin da masu rajin bangaranci, mabarnata, ma’aikata da manyan ‘yan kasuwa a tsawon lokaci suka raba su da shi, har ta kai ga mun fidda tsammanin raya shi, har suka tilasta wa wasu daga cikin ‘yan kasa nisantarsa da kaurace masa, kuma suka nisanci iyalansu, tarihinsu da martarbarsu suka juya masu baya. Sai dai tsayayyu kuma dakakkun matasan nan sun farfado da rura wutar wannan dutsen (volcano) daga can cikin zukatan gabaki dayan ‘yan kasa, sun kuma farkar da wannan makamashin mai karfi, suka kuma hada kan al’ummar kasa waje guda a karkashin kalma guda wacce take ita ce batun ‘yantacciyar kasa wacce take kiyaye alfarmar ‘yan kasarta kuma take nemar masu dukkan farin ciki da dacewa da ci gaba a halin yanzu da kyakkyawar makomarsu a gaba.

Tabbas mun gani daga wajen wadannan matasa abin da yake sanyaya kiraza, yake karfafa zukata kuma yake dawowa da duniya yadda Iraki take tun a asali, kasar da ta kasance ita ce tushe kuma wacce ta assasa dukkan wayewa da yada hasken ilimomi da sani ga dukkan al’ummu, lallai a wajensu mun ga sadaukarwa, jajircewa, farkarwa, iklasi, cikakken tsari da neman hakkokinsu, kangarewa zalunci da barna ta hanyar ruwan sanyi da kaucewa hauma-hauma. Wadannan siffofin abin yabo ba su samuwa ga kowace irin al’umma sai wacce Allah ya karrama ya kuma daukaka sha’aninta, domin ma damar suka yi ganganci, suka mika wuya, suka kaskantar da kawukansu sannan suka karfafi barna da fasadi, to lallai wannan al’umma za ta wulakanta, za ta kaskanta kai hatta mafi karanci na daga hakkokinsu sai an tauye masu shi, kuma wannan shi ne labarin da Annabi (s.a.w.a) ya bayar a cikin hadisi madaukaki: “Babu tsarki da albarka ga al’ummar da a cikinta ba a iya karbarwa rarrauna hakkinsa daga mai iko, koda kuwa ta hanyar daga masa yatsa ne”, (Wasa’ilul Shi’a 16/120.).

Wannan shi ne ainahin abin da nake ta kira zuwa gare shi tun a shekarar 2005, a lokacin da fasadi da zaluncin ‘yan siyasa masu mulki suka bayyana, a lokacin na yi ta kira kan cewa ya kamata al’umma fa ta farka ta fadaka ta nemi hakkokinta ta binciko tushen matsalar da ta dabaibaye jagorancin nan nata.

Ina kira ga hukuma da jagororin siyasa da na soji da su fahimci cewa lallai wadannan matasan a hakikanin gaskia su ne fa arzikin wannan kasar, kuma su ne wadanda za su tsayawa kasar a nan gaba domin ci gabanta, domin haka kada su dinga ketare iyaka a kan wannan tarin arzikin, kuma fa su wadannan matasan su ne dai wadanda suka fuskanci ‘yan ta’adda suka yi gaba da gaba da su har suka ga bayansu suka ‘yanta gabaki dayan duniya daga sharrinsu, sannan su din dai ne suke raya tattakin nan na Arba’in, suka haskaka fuskar Iraki a idon mutanen duniya gabaki dayansu, a saboda haka wajibi ne a saurare su a ji me suke nema ne wai, sannan a hanzarta wajen biya masu bukatunsu har su gamsu su ji cewa suna da fata a rayukansu.

Amma dagewa a kan siyasar tsanantawa da amfani da karfi, to tabbas wannan ba zai haifar da ‘da mai ido ga wannan kasar ba sai dai ma ya kara kwaba lamurran, kuma ku sani lallai da irin wannan ba za ku iya shawo kan wadannan matasan masu hankoron mutuwa da fuskantar harsashi mai rai da kirazansu a bude ba.

Sannan ina mai yin nasiha ga matasa a kan cewa su kiyaye motsinsu da suke yi a cikin ruwan sanyi, su kiyaye dukiyoyin hukuma domin na kowa da kowa ne, da dukiyoyin mutane masu zaman kansu, kuma kada su kaiwa ko da mutum daya daga cikin jami’an tsaro hari ko waninsu, idan har suka kiyaye wadannan to za su samu karin magoya baya na ciki da waje a kan wannan motsin nasu da suke yi, domin gaskiya rushe-rushe da lalata kayayyaki wanda yake wani shiri ne na makiya, kawai zai janyo maku rashin samun goyon baya daga gurin jama’a ne, zai kuma zama sanadin rashin samun hakkokinku, zai canja motsin naku zuwa ga wani aiki na ta’addanci, a saboda haka sai kun kula tare da yin takatsantsan.

Kuma lallai lokaci ya yi da jam’iyyun siyasa da kungiyoyi masu rike da madafun iko su ji kunya, su zo su nemi afuwar ‘yan kasa wadanda suka fito mazansu da matansu, kwansu da kwarkwatarsu da kungiyoyinsu na kwadago suna masu kin wannan salon na tafiyar da mulki mai cike da barna da gazawa wajen iya jagorantar kasar, sannan su zo su ba mutanen kasa wadanda suka cancanta damar daukar nauyin jagorantar kasar.

Wadannan muzaharorin sun fi wadancan akwatunan zaben na zamba wajen bayyanar da manufar ‘yan kasa da bayyanar da zabinsu a fili ga wanda suke son ya wakilce su, ko da kuwa mun sallama cewa wannan hukumar ta zo ne sakamakon kuri’un da ake jefa a cikin akwatuna aka zabe ta, to amma wadannan muzaharorin masu bayyana turjiyar jama’a a fili suna nuna cewa kenan yanzu jama’a sun janye halascin da suka bai wa hukumar, tun da dai su ‘yan kasa dama tun asali su ne tushen mulkin, don haka dole ne a gabatar da abin da suke so a farko kuma ya zama mai dorewa, saboda haka da zarar sun karbe wannan halascin daga mai mulki to fa shi kenan shugabancinsa ya rushe.

 

Muhammad Yakubi – Najaf Mai Tsarki.

1 – Rabi’ul Auwal – 1441 AH.

30 – 10 – 2019 AD.