Lallai ne addini a wurin Allah shi ne Musulunci

| |times read : 1001
Lallai ne addini a wurin Allah shi ne Musulunci
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Da sunansa Madaukaki

“Lallai ne addini a wurin Allah shi ne Musulunci” (Ali Imrana, aya ta 19)[1].

Addini kamar yadda yake a isdilahi wani tsari ne da ya doru a kan imani, dokoki da fikirori wadanda aka kallafa wa dan adam sai kuma daya bangaren wato reshe ko furu’a wato bangaren ayyuka da gabobi, kuma babu makawa ga kowane mutum a wannan duniyar ya zama yana da addini hatta ga mafi koma bayan mutane a jahilci da wauta, sai dai wannan addinin zai iya zama addinin Allah ko na duniya wanda mutum ne a kashin kansa ya kirkire shi, hatta ma wadannan da ake kiransu maguzawa (marasa addini) suna da abin da suka yi imani da shi wato wani fandararren ‘yanci, halasta duk abin da suka ga dama, halatta auren jinsi kai har sukan iya daga yatsa ga kyawawan dabi’u na madaukakin addini.

Kuma ita wannan ayar mai girma (da ta gabata) tana bankado hakikanin wannan dabi’ar ta dan adam, a dalilin haka ne ma sai ba ta tsaya yin nuni a kan cewa tilas ne mutum ya zama yana da addini ba, a’a sai dai kawai kai tsaye tana magana ne a kan mutum ya zama ya san addinin da ya wajaba a gare shi ya yi imani da shi, kuma ya fuskance shi ta yadda zai gina rayuwarsa kacokaf a karkashin koyarwarsa, domin Allah Ta’ala cikin falalarsa, ludufinsa da kaunarsa ga bayinsa bai barsu haka sakakai su dinga shan wahala su karar da shekarunsu suna fadi-tashi wajen neman addinin gaskia ba, a’a bai bukace su da su bata lokaci ba don ya riga ya bayyana masu hanyar da za ta kai su ga dacewa da tsira da fadinsa: “Lallai ne addini a wurin Allah shi ne Musulunci”, ayar ta riga ta togace komai, tun da ga shi tana kore sahihanci da ingancin duk wani addini koda ko mutane sun batawa kansu lokaci wajen kirkirarsa da kirkira masa hukunce-hukunce.

Shi Musulunci ba komai ba ne illa biyayya da sallamawa ga Allah Ta'ala wato wannan a ma’anarsa ta bai-daya kenan, amma a kebantacciyar ma’anarsa to an togace shi ne ga addinin Musuluncin da Annabi (s.a.w.a) ya zo da shi kuma ya zama shi ne cikamakon addinai da Annabta domin shi ne yafi sauran kammaluwa kuma ya fi su daidaito cikin bayyana ma’anar Musulunci wanda ya game dukkan daukacin rayuwa ta daidaiku da ta jama’a a dunkule, kuma babu wani addini da ya game komai da komai kamarsa, Allah ya ce: “A yau na kammala maku addininku, kuma na cika ni’imata a kanku, kuma na yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku”, (Ma’ida, aya ta 3). Wato shi ne addinin da ya wajabta yin imani da dukkan Annabawa magabata da kuma yadda da ingancin abin da suka zo da shi, Allah ya ce: “Ba mu rarrabewa a tsakanin kowanne daga gare su, kuma mu a gare shi masu mika wuya ne”, (Bakara, aya ta 136) da (Ali Imrana, aya ta 84). Sai dai fa bauta wa Allah da yin riko da addini dole ne ya kasance daidai da koyarwar wannan shari’ar ta Musulunci.

Sannan wannan hakikar hankali yana tabbatar da ita haka nan fidirar mutum kuma tana imani da ita ba tare da sun bukaci wani dalili ba, haka nan babu wadanda suke yin shakkar wannan sai masu girman kai; Allah ya ce: “Kuma suka musunta su, alhali zukatansu sun natsu da su saboda zalunci da girman kai”, (Naml, aya ta 14). Kasantuwar Allah shi ne mahaliccin wannan dan adam din kuma shi ne masanin sake-sake da soyace-soyacen zuciyarsa da tsarin halittarsa da dukkan abin da zai gyara masa sha’aninsa, saboda haka a hakikanin gaskiya shi ne wanda ya cancanta ya koma zuwa gare shi don neman sanin abin da zai tafiyar masa da rayuwarsa, da abin da zai kai shi ga daidaito da dacewa.

A cikin waccan surar dai akwai ayar da take karin haske a kan wani dalilin daban wanda zai sa mutum ya rungumi Musulunci koma-bayan waninsa ko wani tsarin da ba nasa ba, Allah Ta'ala ya ce: “Shin wanin addinin Allah suke nema, alhali kuwa a gare shi ne wadanda suke cikin sama da kasa suka sallamawa a kan suna so ko suna ki, kuma zuwa gare shi ake mayar da su?” (Ali Imarana, aya ta 83). Don haka gabaki dayan samuwa mai sallamawa ce ga abin da Allah Ta'ala yake so da yadda ya nufa, kuma suna tafiya ne daidai da yadda Allah ya tsara su ya kuma dora su a kai, shi kuwa mutum ba komai ba ne sai wata ‘yar mitsitsiyar halitta a cikin wannan duniyar kuma mai kaskantar da kai ga tsarin Allah domin ko an haife shi a wannan shakalin da tsarin yadda yake a surarsa din nan ba tare da wani iko daga gare shi ba, kuma yana girma, yana tsufa, ya mutu haka nan kuma gabobin jikinsa suna ayyuka daban-daban ba tare da wata kudura daga gare shi ba, a saboda haka wannan Musuluncin da wannan sallamawar ta dole ba makawa dole ne ya gwama ta da sallamawa ta shari’a domin motsinsa ya dace da wannan duniyar gabaki dayanta, Allah ya ce: “Kuma wane ne ya fi kyautatuwa ga addini daga wanda ya sallama kansa ga Allah, alhali yana mai kyautatawa”, (Nisa’i, aya ta 125). Da zarar bai yi hakan ba zai fadawa fitintinu da wahalhalu ne kawai.

Kuma lallai daga baya-bayan nan ilimin kimiyya ya binciko wannan, don kuwa ya tabbatar a kan cewa idan mutum ya fitar da kansa daga tsarin halitta na dabi’a to zai janyo wa kansa tabarbarewa da halaka ne, to kuma haka lamarin yake hatta ga zamantakewar mutane da dauloli.

Tambaya a nan ita ce “Shin wanin addinin Allah suke nema”? Tambaya ce da a cikinta akwai nau’i na tsawatarwa, musuntawa da tuhuma ga wanda ya fitar da kansa daga cikin wannan tsarin na kaunu (tsarin dabi’a) wanda yake shi ne a kan daidai, to don haka ne ma amsar da ta biyo bayan ayoyin nan guda biyu suka bayyana sakamako mai radadi ga irin wannan fita din, "Kuma duk wanda ya nemi wanin Musulunci ya zamar masa addini, to ba za a karba daga gare shi ba, kuma shi a Lahira yana daga cikin masu asara”. (Ali Imrana, aya ta 85). A saboda haka duk wanda ya nemi yin wani addini sabanin Musulunci to ya yi asara domin ya saki wannan babbar hanyar ta arziki wacce Allah Ta'ala ya yi masa baiwarta ya canja masa ita da wahamomi da bata, amma sai ya karar da shekarunsa masu kima cikin jin wani kaskantaccen dadi da bin son ransa da girman kai, dangane da wannan ne Amirul Muminina (as) yake cewa: “Kuma duk wanda ya nemi wani addini sabanin Musulunci ya zamar masa addini, to tabewarsa ta tabbata haka kuma albarkar rayuwarsa ta yanke, kura-kuransa sun girmama sannan karshensa zai kasance cike da bakin ciki mai tsawo da azaba mai tsanani, kuma ni ina mai tawakkali ga Allah, irin tawakkalin mai komawa zuwa gare shi kuma ina neman shiriya daga gare shi wacce za ta zarce da ni zuwa Aljannarsa wacce a cikinta ake samun kwadaitarwarsa da yardarsa”[2]. Da kuma fadinsa (as) “Ya ku mutane! Addininku! Addininku! Ku yi riko da shi, kada wani ya kawata maku wani abu can daban, kada wani ya juyar da ku daga gare shi, ku sani sabon Allah a cikinsa ya fi kyautatawa a cikin waninsa, domin sabon da aka yi a cikinsa ana gafarta shi, amma ba a karbar kyautatawar da aka yi a cikin waninsa”[3].

To ku mu lura da wannan hakikar, ma damar muna cikin duniyar nan to akwai damar yin aiki don kofarsa a bude take a gabanmu don haka mu yi riko da addininmu mu sanya shi mafi muhimmanci a kan komai a gare mu, in ko ba haka ba da sannu hakika za ta bayyana ga gafalallu a ranar kiyama a yayin da nadama ba za ta yi amfani ba “Kuma shi a Lahira yana daga cikin masu asara”. (Ali Imrana, aya ta 85). A wannan lokacin ne maguzawa da masu inkarain samuwar Allah da ‘yan addinin gargajiya za su san wane ne zai yi nasara ya samu babban rabo?

Kuma dole ne mu kara lura a kan cewa Musulunci fa ba kawai mujarradin furta kalmar shahada ba ne, haka nan ma sauke nauyin ibadar da ta wajaba wacce ta takaita ga mutum shi kadai ba ta wadatarwa, domin imani da biyayya ba su hakkakuwa ko samuwa da wannan din shi kadai, a’a sai dai ta hanyar dabbaka gabaki dayan shari’a da kuma lazimtuwa da addini a cikin dukkanin sha’anonin rayuwa, wannan kuma shi ne Musulunci, ba abubuwa na zahiri ko wasu gurbatattun littafai da makamantan haka wadanda aka watsar da su a cikin zawiyoyi da koguna ba. Domin a gaskiya daga cikin muhimman alamomin riko da addini akwai batun raya shi da kuma yada shi da kiran sauran mutane zuwa gare shi, akwai wata ruwaya da aka samu daga Imam Bakir (as) ya ce: “Babu addini ga wanda bautarsa ga Allah ba ta kai shi ga yin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna ba”[4]. Haka nan ma Amirul Muminina (as) ya zargi masu sakaci da addini wadanda suka mayar da addinin abin neman duniyarsu inda ya ce: “Addinin dayanku ya zama a kan harshe kawai (bai kai zuci ba), kamar wanda ya gama aikinsa yana jiran sakamako ko yardar mai gidansa[5]. Wato dai saboda karancin ba da muhimmanci ga addininku ya sanya kuna jin kun wadatu daga Mahaliccinku kun gamsu a kan yadda ku ke din nan, don haka ba ku da wata bukata ta yin wani aiki, alhali sam-sam lamarin ba haka yake ba. An samu wata ruwaya daga Imam Ali (as) cewa: “Idan ka sanya addininka ya zama koma-bayan duniyarka to ka halakar da addininka da duniyarka, kuma a Lahira za ka kasance daga cikin masu asara, (amma) idan ka sanya duniyarka ta zama mai bin addininka to ka ‘yanta addininka da duniyarka, kuma a Lahira za ka kasance daga cikin masu rabauta”[6].

To kuma lallai Qur’ani mai girma ya bai wa addinin nan daraja mai tarin girma ya kuma sanya shi a gaba ga dukkan komai da komai, Allah Ta'ala ya ce: “Kuma fitina ita ce mafi tsanani daga kisa”. (Bakara, aya ta 191). “Kuma fitina ita ce mafi girma daga kisa”, (Bakara, aya ta 217). Don haka kisan kai babu gaira babu dalili yakan yi sauki ne albarkacin riko da addini da kuma nesantar da shi (addinin) daga fitina. An ruwaito daga Imam Sadik (as) a cikin tafsirin fadin Allah Ta'ala: “Sai Allah ya tsare shi daga munanan abubuwan da suka yi na makirci”, (Gafir, aya ta 45). To sai ya ce: “Ai ana nufin muminin nan na Ali-Fir’auna. Ina rantsuwa da Allah sun daddatsa shi gunduwa gunduwa, sai dai Allah ya tsare shi don kuwa bai fitinu ya bar addininsa ba”[7].

Dangane da wannan akwai ruwayoyin Ma’asumai (as) da aka ruwaito, an samu daga Amirul Mumina (as) ya ce: “Duk lokacin da wata matsala ta tunkaro addininku to ku bayar da rayukanku domin ceton addinin naku, kuma ku sani lallai halakakke shi ne wanda ya rasa addininsa kuma wanda aka yiwa wasoso shi ne wanda addininsa ya subuce masa”[8].

Kuma lallai wadanda Allah Ta'ala ya yi masu muwafaka sun fahimci wannan hakikar (don haka) sai suka yi riko da addininsu riko na hakika gam-gam duk da irin cutarwar da aka yi masu da kuma azabtarwa mai tsananin gaske duk dai domin su bar addinin (amma ba su bari ba), Qur'ani mai girma yana bayar da labarin kissar wasu daga cikinsu kamar mutanen Ukhdud, wadanda aka tona wagegen rami aka rura wuta aka jefa su ciki amma tare da haka suka dake a kan imaninsu da addininsu ba su sallama wa azzalumai ba, Allah ya ce: “Kuma ba su tuhumce su ba, face sai don sun yi imani da Allah Mabuwayi, wanda ake godewa”. (Buruj, aya ta 8). Haka ma masu sihirin Fir’auna wadanda ya tsoratar da su da cewa zai yanke hannaye da kafafuwansu bayan nan zai kashe su, to amma sai suka ba shi amsa da cewa: “Sai dai ka hukunta abin da ka ke mai hukuntawa, iyakar hukuncin da za ka iya yi a wannan rayuwar duniyar ne kawai. Lallai ne mu, mun yi imani da Ubangijinmu domin ya gafarta mana laifukanmu” (Da Ha, aya ta 72-73). Haka nan kuma akwai kissar Asiya matar Fir’auna wacce ba ta karaya a gaba ga azabtarwar Fir’auna ba kawai ma sai ta kama rokon Allah Ta'ala tana cewa: “Ya Ubangiji ka gina mani wani gida a wurinka a Aljanna kuma ka tseratar da ni daga Fir’auna da aikinsa” (Tahrim, aya ta 11). Haka nan ma akwai As’habul Kahfi wadanda duk da matsayinsu na shuwagabanni a masarautar Romaniya amma hakan bai rude su ba, kuma wani abu daga kamun Romawa bai ba su tsoro ba, Allah ya ce: “A lokacin da suka tsayu, sannan suka ce Ubangijinmu shi ne Ubangijin sammai da kasa, ba za mu kirayi waninsa abin bautawa ba, (idan muka yi haka) lallai ne hakika mun fadi abin da ya ketare haddi” (Kahfi, aya ta 14).

To a gefe guda kuma, akwai asararru masu yawan gaske wadanda shaidan da duniya suka rudar da su, misali akwai alkalin alkalai na daular Abbasiyawa – wanda yake shi ne babban malamin addini mafi girma a daular –   shi ne ya yi ta kai-komo wajen Mu’utasim Abbasi don ganin an kashe Imam Jawad (as) bisa hassadar cewa Mu’utasim din ya yi aiki da hukuncin da Imam (as) din ya yanke a kan yanke hannun barawo, tare da yasan cewa wannan aikin nasa zai kai shi wuta.

Sannan akwai irinsu Humaid bn Kahtaba gwamna kuma kwamanda a daular Abbasiyawa wanda a cikin ruwayar da za ta zo (nan gaba) wacce ta tona asirin wani bangare na aikin dabbancin Banul Abbas a kan Ahlul Baitin Annabta da tsanantawar dawagitai da shaidanun aljanu da mutane gare su irin yadda suka juyawa addini baya da kuma rashin dogararsu da shi, an samu a cikin littafin Akhbaril Ridha na shaikh Saduk da sanadinsa daga Ubaidullah Bazzar Al- Naisaburi – wanda ya kasance dattijo ne – ya ce: “Ya kasance cewa akwai wata mu’amala da ta shiga tsakanina da Humaid bn Kahtaba Al- Ta’i, to wata rana sai na tafi wajensa, sai labari ya je masa cewa na zo, sai ya yi mani iso a daidai lokacin da ko kayan da suke jikina wadanda na yi tafiyar da su ban canja ba, wannan ko ya kasance cikin watan Ramadan ne lokacin sallar azahar. To da na shiga wajensa sai na same shi a cikin gidan da ruwa ne ke gudana a cikinsa, sai na yi masa sallama sannan na zauna, sai aka zo da tasa da kuma buta sai ya wanke hannunsa a ciki, sannan ya umarce ni da in wanke hannuna, sannan sai aka kawo kwanon abinci, to kawai na manta cewa azumi nake yi, kuma yanzu muna cikin watan Ramadan ne, to sai na tuna don haka sai na tsame hannuna daga cin abincin, sai Humaid ya ce mini: Me ya faru kuma ka daina ci? Sai na ce masa: Ya shugaba wannan ai watan Ramadan ne, kuma ni ba marar lafiya ba ne, kuma ba na tare da wata lalurar da za ta hana ni yin azumi, amma watakila shi shugaba yana da wata lalura ce wacce ta hana shi yin azumin, to sai ya ce: Ba ni da wata lalurar da ta hanani yin azumi, kuma jikina kalau yake, sannan sai idanunsa suka cika da kwalla har ya fashe da kuka. To bayan ya kammala cin abincinsa sai na ce masa: Mai ya sa ka kuka ya kai shugaba? Sai ya ce: A wani dare a lokacin Harun[9] Al-Rashid yana Tus, ya aika min wani hadimi ya kirani, to da na shiga wajensa, na same shi rike da fitila da koren takobi an zare shi daga kubensa a hannunsa, hadiminsa kuma yana tsaye a gefensa, lokacin da na karasa na tsaya a gabansa sai ya dago kansa ya ce mani: Yaya matsayin biyayyarka ga shugaban muminai take (shi Harun yana nufin kansa)? Sai na ce: Zan maka biyayya da raina da dukiyata, to sai ya sunkuyar da kansa kasa sannan ya ce: To kana iya tafiya. Sai na tafi gida, ba tare da jimawa ba sai ga hadimin nan ya sake dawowa wajena ya ce: shugaban muminina yana kiranka. Sai a raina na ce: Daga Allah mu ke, amma fa ina cikin tsoron kada dai mutumin nan yunkurin kashe ni yake yi amma da ya ganni ne sai ya ji nauyina, to dai sai na koma wajensa, sai ya sake dago kansa ya kalleni ya ce mani: Yaya matsayin biyayyarka ga shugaban muminai take? Sai na ce masa: Zan yi maka biyayya da dukiyata da raina da dana da na haifa, sai ya yi dariya – domin shugaban ya san cewa Kahdaba ya fahimci sakonsa sarai kuma ya san abin da ake nema a wajensa ya wuce gaban wannan – Sannan sai ya ba ni izinin tafiya. Bayan na koma gida ba da jimawa ba kuma sai ga dan sako ya sake dawowa ya ce: Ka zo shugaban muminai yana kira, to sai na tafi zuwa gare shi, alhali yana nan tsaye a yadda yake tun a farko, sai ya dago kansa yana kallona sannan ya ce: Yaya matsayin biyayyarka ga shugaban muminai take? Sai na ce: Zan yi maka biyayya da dukiyata da raina da iyalaina da dan cikina da addinina gaba-daya, sai ya yi dariya, sannan ya ce: Amshi wannan takobin kuma ka aikata abin da wannan hadimin ya fada maka.  Ya ce: Sai hadimin ya karbi takobin ya miko mani, ya tafi da ni wani gida wanda kofarsa take a kulle, sai ya bude kofar sai ga rijiya a tsakar gidan, da dakuna guda uku wadanda kofofinsu suke a kulle, sai ya bude kofar daya daga cikin dakunan nan, sai ga mutum ashirin a cikinsa gashin kansu ya yi zaro-zaro, farcensu kuma sun yi zako-zako, ga su nan tsofaffi ne da matasa duk an daddaure su da sarka. Sai hadimin ya ce mani: Shugaban muminai ya umarce ka da ka kashe wadannan, mutanen nan fa dukkansu Alawiyyawa ne ‘ya’yan Ali da Fatima (as). Sai ya dinga fito min da su daya bayan daya har zuwa na karshensu, sannan sai ya tura jikkunansu da kawukansu cikin rijiyar nan. Sannan ya bude kofar daki na biyu, sai ga mutane ashirin a cikinsa shi ma kuma dukkansu Alawiyyawa, ‘ya’yan Ali da Fatima (as) suna daddaure da sarka. Sai ya ce mani: Shugaban muminai ya umarce ka da ka kashe wadannan, sai ya dinga fito min da su daya bayan daya ina sare masu kawuka, shi kuma yana jefa jikin da kan cikin rijiya, har na zo kan na karshensu. Sannan sai ya bude kofar daki na uku, a nan din ma kwatankwacin abin da ke wadancan dakunan ne wato mutum ashirin dukkansu Alawiyyawa, ‘ya’yan Ali da Fatima (as) suna daddaure da sarka, gashin kansu ya yi zaro-zaro, faratansu kuma sun yi zako-zako. Ya ce: Shugaban muminai dai ya sake umartarka da ka kashe masa wadannan. Sai ya dinga fito min da su daya bayan daya ina tsinke kawukansu shi kuma yana jefa su cikin wannan rijiyar har na isa kan mutum na ashirin da tara daga cikinsu, sai mutum daya wani dattijo wanda gashi ya yi masa buzu-buzu, sai ya kalle ni ya ce: Amma kai kam ka tabe ka yi asara, wai kai wane irin uzuri ne ka ke da shi a ranar gobe Kiyama idan aka kawo ka gaban kakanmu Manzon Allah (s.a.w.a), alhali ka kashe masa ‘ya’yansa wadanda Ali da Fatima (as) suka haifa har mutum sittin? To sai hannayena suka fara karkarwa jikina ya yi sanyi. Sai wannan hadimin ya kalleni a fusace ya daka mani tsawa, sai kawai na dan matsa kusa da wannan dattijo shi ma nan take na tsinke kansa, shi kuma hadimin ya jefar da shi cikin rijiyar nan. To ni da na aikata wannan danyen aiki, na salwantar da rayukan ‘ya’yan Manzon Allah (s.a.w.a) har guda sittin, wane amfani azumi da sallah za su yi mani, alhalin bana shakkar zan dawwama a wutar jahannama”[10].

Ita kuma waki’ar Karbala ta kunshi nau’oin mutane kashi biyu ne, bangaren farko Hur Al- Riyahi wanda yake cike da firgici alhali yana kallon rundunar Bn Ziyad suna tunkarowa da nufin kashe Imam Husain (as) da Ahlul Baitinsa, shi ya sanya ma da abokinsa ya tambaye shi mene ne ya sabbaba masa wannan firginci sai ya ce: “Wato ina da zabi ne tsakanin Aljanna da wuta, kuma ga shi ban zabarwa kaina komai daga Aljannar ba”.

Bangare na biyu kuma Umar bn Sa’ad bn Abi Wakkas, shi wannan Ba-Kuraishe ne kuma yana da dangantaka ta jini da Imam Husain (as) sannan ya sanshi farin sani, sai don son kansa da kwadayinsa da karkatarsa kan ya zama gwamnan birnin Rai da Gurgan su ne suka tunkuda shi zuwa ga wannan mummunar ta’asar wacce ta zama sanadiyyar asararsa ta duniya da Lahira, alhali a daren da yake shirin ya yanke hukunci shin ko ya auka wa Imam ne ko a’a, to sai da ya dinga yin taraddudi a kan hakan:

Shin zan hakura da mulkin birnin Rai kuwa alhali shi ne babban burina.

              Ko zan koma ina a matsayin abin zargi da zunubin kashe Husain.

Husain dan baffana ne fa, amma abubuwan (da zan samu) suna fa da yawa.

            Ina rantsuwa da rayuwarka mulkin birnin Rai sanyin idaniyata ne.

 

  

 



[1] - An gabatar da wannan muhadara a ranar Juma’a 19 ga watan Rabiul Auwal 1439 AH daidai da 1/12/2017 AD.

[2] - Nahajul Balaga, Huduba ta 161, wacce tana daga cikin hudubobinsa a kan siffar Annabi (s.a.w.a) da Ahlul Baitinsa (as) da mabiyansa wacce a ciki ya yi wa’azi da a ji tsoron Allah. 

[3] - Al- Kafi, mujalladi na 2 shafi na 464.

[4] - Biharul Anwar 100/86 Hadisi na 59.

[5] - Nahajul Balaga, Huduba ta 113.

[6] - Gurarul Hikam, 3750 – 3751.

[7] - Biharul Anwar, 13/162, Hadisi na 2.

[8] - Al- Kafi, 2/216 Hadisi na 2. 

[9] - Watakila ya yi kuskure ne, domin mafi inganci shi ne cewa Abu Ja’afar Al- Mansur ne domin Bn Kahdaba ya rasu ne a zamanin da ke kusa da zamanin rasuwar Mansur Abbasi.

[10] - Uyunu Akhbaril Ridha (as), mujalladi na 1, shafi na 108, sai Biharul Anwar 48/178.