Bayanin Karshe Na Ziyarar Arba’in Ta Miliyoyin Jama’a

| |times read : 467
Bayanin Karshe Na Ziyarar Arba’in Ta Miliyoyin Jama’a
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Bayanin Karshe Na Ziyarar Arba’in Ta Miliyoyin Jama’a

Godiya ta tabbata ga Allah wanda ba shi da abokin tarayya, kuma godiya ta tabbata a gare shi kamar yadda ya cancanta a yi masa godiya mai tarin yawa, tsira da amincinsa su tabbata ga shugaban halitta gabaki dayanta wanda yake shiryarwa zuwa ga gaskiya mabayyaniya, Abul Kasim Muhammad bn Abdullah da Alayensa masu tsarki da tsarkaka.

Aminci ya tabbata a kan Husain da Aliyu bn Husain da ‘ya’yan Husain da sahabban Husain wadanda suka tsaya tsayin daka domin kariya ga Imam Husain (as).

Muna yin ta’aziyyar tunawa da zagayowar kwanaki arba’in na shahadar Imam Husain (as) ga musulmai da ma’abota ‘yanci na duniya gabaki dayansu, musamman dai wadanda suka niko gari daga sassa daban-daban na duniya domin su ziyarci mashhadodi masu tsarki na Imamai (as) domin su bayyanar da kyawawan halaye na kawo gyara, ‘yanci, kamala da kuma dukkan asasi mai kyau kuma madaukaki na ‘yan adamtaka, sannan kuma suna masu barranta daga dukkan nau’oi na zalunci, fasadi, kaucewa daga hanya, dagawa da keta.

Haka nan muna taya al’ummar Iraki murna – maukibobinsu, kungiyoyinsu, bangarorinsu, mu’assasoshinsu da daidaikunsu – a kan irin wannan tsayin dakan nasu mai girma mai cike da tawali’u, sadaukarwa da kauna duk dai domin ganin cewa wannan ibadar mai albarka an yi ta cikin nasara daga dukkan janibobinta, ta yadda ku din nan a miliyoyinku dunkule waje guda ku ka tsayu wajen ganin kun hidimtawa dukkan masu ziyara ba tare da kun bar mutum daya cikin wata bukata ba, wanda wannan wani abu ne da ya cika gabaki dayan duniya da mamaki.

Wannan lamari mai girma bai kasance mai samun nasara da bunkasa irin haka ba sai domin wannan kokarin mai albarka ba, don haka suna da rabo mai tsoka na karamci da madaukakan mukamai wadanda Allah Tabaraka wa Ta'ala ya tanadarwa maziyarta Imam Husain (as), domin haka ina ganin bai dace ba a ce an gama wannan munasaba ba tare da an yi godiya ta musamman gare su gabaki dayansu ba.  

Tabbas wanda duk ya bayar da irin wannan kyauta ga Imam Husain (as), to lallai Allah ba zai wofintar da su ba kuma ba zai tozarta kyautatawarsu ba, Allah ya ce: “Lallai ne Allah ba ya tozarta ladar masu kyautatawa”, (Kahafi, aya ta 30). Kuma Allah zai ba su mafita a cikin lamurransu, sannan kuma a albarkacin raya wannan munasabar ta tunawa da lamarin Husainiyya Allah zai yaye masu zaluncin azzalumai da fasadinsu kamar yadda albarkacin hakan ya yaye masu zaluncin wadanda suka gabata.

Kuma ni na yi imanin cewa wannan kwazon wanda ke cike da iklasi yana faranta ran Imaminmu Imam Mahdi (Tsiran Allah da amincinsa su tabbata a gare shi), kuma zai zama sanadin gaggautowar bayyanarsa mai albarka, kuma shi Imam (as) yana ganin miliyoyin ‘yan shi’arsa wadanda suke zuwa daga gomomin kasashe suna masu tattaruwa a makwancin (kabarin) kakansa shugaban shahidai (as). Suna masu ‘yanta kawukansu daga dokin sha’awa, kaskanci, bangaranci da jahilci, don haka ya hau kanmu mu ci gaba da kokartawa domin samun nasara a kan zukatanmu masu umarni ga mummunan aiki da kuma a kan shaidanun aljanu da mutane.    

Lallai wani babban abin lura shi ne rashin ganin ‘yan siyasa da shuwagabannin jam’iyyu a wannan tattaki wanda maziyarta suke gudanarwa da kuma rashin zuwansu domin su hidimta wa maziyartan ta hanyar raba masu abin da za su ci da sauransu wanda wannan yana kara bayyana irin makircin da suke kullawa na yaudarar mutane don su samu damar ci gaba da fasadi da salladuwa a kan jama’a, wannan kuma wani abin kunya ne daga gare su kuma su da kansu sun fahimci hakan domin sun gane cewa yanzu fa al’umma ta farka ba za ta yadda da zalunci ba kuma ba za su sake yadda a dinga yin wasa da kwakwalensu ba, kuma ba za su yadda su dinga fakewa a bayan abubuwa masu tsarki suna shirga masu karairayi ba. Wadannan mutanen laifukansu ga Musulunci sun girmama, wata daddadar maganarsu da alkawuransu na karya cewa wai za su kawo gyara wadanda suka zama sanadin bude masu sababbin hanyoyi na barna da satar dukiyar al’umma ba za su kwace su ba.

Ranar da wadannan miliyoyin jama’ar za su kawar da zalunci da barna daga tushensu ba ta da nisa, musamman bayan samun wannan baiwar ta yin tattaki zuwa makwancin uban ‘yantattu kuma shugaban shahidai Imam Husain (as) wanda yake shi ne hakikanin mai kawo gyara, mai neman ‘yanci da samar da rayuwa mai karamci, mai kin kaskantarwa, wulakantarwa, bautarwa, cin fuska da tozartawa, idan dai har azzaluman mabarnatan nan ba su dawo suka tuba suka kyautata tubarsu ta hanyar yin ayyuka tukuru suka dawo rakiyar barna suka jagoranci al’ummar Iraki masu girma da gaskiya ba.

Lallai jagorancin addini mai shiryatarwa da Hauzar ilimi ta addini madaukakiya ba za su sanya ido suna kallo a kan idonsu ana yanka mutanen kasa da takobin talauci, cusgunawa, rashin aikin yi, fasadi, barna, jahilci da rashin lafiya kai hatta ma da kisan kai ta hanyar harsashi mai rai ba, don haka suna ganin wajibi ne da ya hau kawukansu su daga muryoyinsu tare da sauran jama’a don warware masu hakkokinsu na shari’a ta hanyar lumana wacce tsarin mulki ya ba su da dukkan dokokin ‘yancin dan adam tare da kauracewa duk wani kai hari a kan kadarori gwamnati da na masu zaman kansu.

Sannan kuma wajibi ne a kan shugabannin kasa su yi aiki cikin hikima kuma su saurari kira na hankali da mutuntaka tare da biyan bukatun jama’a domin samun ingantacciyar hanyar warware matsalolinsu na yau da kullum sannan su samar da tsare-tsaren wasu dabaru wadanda za su kawo karshen wannan gwamnatin mai cike da fasadi wacce take tsaye a kan barna tun daga tushenta, kuma su guji siyasar makirci, cin amana da tuhumce-tuhumcen ma’aikata da dai sauransu. Wannan ne ya jawo abin nan da babu mai iya gaskata shi a ce matasan da ba su dauke da komai amma su iya fitowa kan tituna suna fuskantar harsasai masu rai gaba da gaba.

Muna sake nanata kiranmu na a kafa majalisar kwararru da masana a dukkan fannonin rayuwa, kuma Iraki cike take da ire-iren wadannan, domin majalisar ta dinga lura da matsalolin kasa da burace-buracen matasa tana bayar da mafita mai kyau a kai a halin yanzu da kuma a nan gaba, su kuma ‘yan siyasa masu rike da madafun iko dole ne su dinga saurara wa majalisar tare da neman shawararsu da kuma karbar ra’ayoyinsu. Amma yin tafiyar hawainiya cikin lamarin wanda ya yi kama da ana zuba toka a idanu ne kawai ba zai taba gamsar da wanda yake son ya samu rayuwa mai karamci ba.

Allah Ta'ala ya ce: “Kuma idan ku ka juya (daga yi masa da’a) zai musanya wadansu mutane wadanda ba ku ba sannan kuma ba za su kasance kwatankwacinku ba”, (Muhammad, aya ta 38).

Muhammad Yakubi.

20 ga Safar mai alheri 1441 AH.

Daidai da 19-10-2019 AD.