Arba’in Mai Dauke Da Budi…… Daga Ashura Zuwa Arba’in

| |times read : 492
Arba’in Mai Dauke Da Budi…… Daga Ashura Zuwa Arba’in
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Da Sunansa Madaukaki

Arba’in Mai Dauke Da Budi…… Daga Ashura Zuwa Arba’in

An samo daga Imam Sadik (as) ya ce: “Yayin da tsananin azaba ya tsawaita ga bani Isra’la… Sun yi kururuwa da kai kukansu ga Allah tsawon asubahi arba’in, to sai Allah ya aika zuwa ga Musa da Harun (as) kan cewa su tseratar da su daga Fir’auna, sai Allah ya kiyaye su tsawon shekaru saba’in, to haka kuma da za ku aikata irin wancan da Allah ya kawo mana budi daga gare shi, amma idan har ba ku aikata ba to lallai lamarin sai ya dangane iyaka danganewa”[1].

Don haka wani bangare na gaggautowar bayyana, nasara da kafuwar mulkin Waliyin Allah mafi girma (as) da wani bangare na sabubbansa suna a hannunmu ne, kuma har ga shi ma Imam Sadik (as) yana kiranmu a kan mu tsayu da wajibin da ke kanmu a kan mu yunkura domin gaggautowar bayyanarsa da kafuwar mulkinsa da yada shiriya, gyara da adalci a tsakanin mutane, kuma mu yunkura domin ganin mun tseratar da su daga zalunci, keta, kiyayya da danniya ta hanyar yin kururuwa da kai kukanmu ga Allah Ta’ala tare da kaskantar da kai da tawassuli domin ya gyara mana abubuwan na daga ayyukanmu albarkacin tausayinsa, kuma idan har ba mu aikata hakan ba to lallai hukunci zai gudana gare shi da gare mu, kamar  dai yanzu yadda muke ciki kuma ba za a samu canji mafi kyau ba, mu ne kuma ababen tambaya ga halin da yake gudana gare su kuma su (su Imam ‘as’) masu sallamawa ne ga al’amarin Allah Ta’ala a kowane hali.

Wadannan kwanukan Arba’in din da suke da alaka da Imam Husain (as) wadanda suke farowa daga Ashura zuwa ziyarar Arba’in, kwanuka ne arba’in da suka dace da mu kai kukanmu da kaskantar da kanmu ga Allah domin alakar da ke tsakanin yunkurin Imam Husain (as) da daular adalci ta Ubangiji, wacce take zo wa da dukkan alheri kuma tushe ce ta samun karfi a hannun masu shiryatarwa kuma masu kawo gyara. To lallai wadannan kiraye-kirayen sun cancanci amsawa, don kuwa da sannu gomomin miliyoyi za su fuskanci makwancin (Imam Husain (as)) mai tsarki suna masu ziyartarsa, ko suna masu raya majalisosi masu albarka na tunawa da shi a gabaki dayan sassan duniya, kuma lallai addu’a a karkashin kubba din Imam Husain (as) da majalisosin tunawa da lamarinsa da wuraren taron miliyoyi karbabbiya ce, cike da zukata masu imani (da a kan gabobin da suka yi sa’ayi domin zuwa wuraren bautarka suna masu da’a gare ka, kuma suka yi ikirari a kan neman gafararka) [2], a wurare masu tsarki da madaukakan lokuta a kan neman al’amari, da fatan zai gaggauta amsawa.

Kuma mun sani cewa mujarradin mi-mi-mi da baki da nufin muna yin addu’a shi kadai ba ya wadatarwa madamar ba a gwama shi da iklasi da gaskiya ba, tare da canja zukata zuwa mafi dacewa, da himma wajen gyaran kawukanmu a daidaikunmu da kuma a jama’a kamar yadda ya zo a wasiyyar Annabi (s.a.w.a): “Ku sallamawa Allah Ubangijinku da niyyoyi magaskata masu tsarki ko ya datar da ku”[3].

 

Muhammad Al-Yakubi – Najaf Mai Tsarki

Daren 9 Muharram 1441 AH

Daidai da 9/9/2019 AD 

 



[1] - Tafsirul Ayashi, 2/ 154 Hadisi 49.

[2] - Wani bangare na Addu’ar Amiril Mumina (as) wacce aka fi sani da Du’au Kumail.

[3] - Daga cikin Hudubar Annabi (s.a.w.a) a Juma’ar karshen Sha’aban.