Wasici A Kan Neman Ilimi / 29
09/07/2020 17:50:00 |
17/ZULKI’IDA/1441|times read : 502
Wasici A Kan Neman Ilimi / 29
Kwadaitarwa da muhimmantarwa ga yin karatu da neman ilimi da ma’arifa wani kira ne na musamman kuma na din-din-din da Qur’ani mai girma yake yi, sannan lamari ne da Allah Ta’ala ya ladabtar da Annabinsa (s.a.w.a) a kai: {Kuma ka ce: Ya Ubangiji ka kara mini ilimi} (Suratu Da Ha, aya ta 114). Haka nan ma ya zo a hadisin Annabi (s.a.w.a): “Da za a wayi gari wani yini ya zo min amma ban karu da ilimi a cikinsa ba – ilimin da zai kusantar da ni ga Allah – (to da sai in ce) kada Allah ya albarkaci hudowar ranar wannan yinin”.