Sallamawa Ga Manzon Allah A Gurin Neman Ilimi / 17
09/07/2020 17:50:00 |
17/ZULKI’IDA/1441|times read : 505
Sallamawa Ga Manzon Allah A Gurin Neman Ilimi / 17
Annabi (s.a.w.a) duk da girman matsayinsa amma ya kasance yana neman karin ilimi a kowane lokaci tare da yin addu’a: (Allah ka amfanar da ni abin da ka sanar da ni, kuma ka sanar da ni abin da zai amfane ni, kuma ka kara min ilimi), mu kuma an riga an hore mu da mu mika wuya ga Manzon Allah (s.a.w.a), tare da cewa mu ne ya fi kamata mu nemi ilimi da karinsa a kowane lokaci da zamani, a don haka mutum zai ci gaba da neman ilimi ne koda wane irin matsayi ya taka na ilimin.