Al-Kur’ani yana haskaka hanyar shiriya / 10

| |times read : 494
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Al-Kur’ani yana haskaka hanyar shiriya / 10

Idanu ba sa iya ganin abin da ke kewaye da su sai idan haske ya haska gurin sai hasken ya ratsa idanun, to sai su dinga gani garau, wannan kuma shi ne irin rawar da Kur’ani yake takawa domin yana haskaka hanyar shiriya, imani, dacewa da sa’ada ne; {Shin kuma wanda ya kasance matacce sannan muka rayar da shi kuma muka sanya wani haske gare shi yana tafiya da shi, zai zama misalin wanda yake cikin duffai, kuma shi ba mai fita ne daga gare su ba…} (Suratul An’am/ aya ta 122). A saboda haka wanda ya shiriya da haskensa to yana daga cikin masu rabauta.