Kwadaitarwa ga muminai mazauna garuruwa daban-daban a kan su ziyarci Najaf mai Tsarki a ranar Ghadir.

| |times read : 528
Kwadaitarwa ga muminai mazauna garuruwa daban-daban a kan su ziyarci Najaf mai Tsarki a ranar Ghadir.
  • Post on Facebook
  • Share on WhatsApp
  • Share on Telegram
  • Twitter
  • Tumblr
  • Share on Pinterest
  • Share on Instagram
  • pdf
  • Print version
  • save

Kwadaitarwa ga muminai mazauna garuruwa daban-daban a kan su ziyarci Najaf mai Tsarki a ranar Ghadir.

 

Bismihi Taala

Kwadaitarwa ga muminai mazauna garuruwa daban-daban a kan su ziyarci Najaf mai Tsarki a ranar Ghadir.

Muna kwadaitar da muminai maza da mata a kan su ziyarci Imam Ali (as) a birnin Najaf mai tsarki a wannan munasaba ta Idin Ghadir, suna masu amsawa ga kiran A’imma (as) ta bakin Imam Ridha (as) a lokacin da yake fadawa daya daga cikin sahabbansa makusanta: (Ya kai dan Abi Nasr duk inda ka samu kanka to a ranar Ghadir ka halarci makwancin Amirul muminina (as), domin lallai Allah yana yafewa dukkan mumini da mumina, musulmi da musulma zunubbansu na shekaru sittin, haka kuma yana ‘yanta bayinsa daga wuta kwatankwacin rabin wadanda ya ‘yanta  a watan Ramadan, daren lailatul Kadar da daren sallah, haka nan ma yana sakawa duk wanda ya yi kyautar dirhami daya ga ‘yan uwansa ma’abota sani da dirhami dubu (Al-Tahzib Na Shaikh Dusi 6/4).

 

Shi kuma wannan kira din wanda a cikinsa aka yi amfani da kalmar (duk inda ka samu kanka) a sarari ba tare da kaidi ba, to ana fuskantar da kiran ne zuwa ga kowa da kowa ba tare da togaciya ba wato dukkanin mutanen gabacin duniya da na yammacinta, sai dai mutumin da yake da wani karbabben uzuri, to shi wannan sai ya karanta ziyararsa daga nesa.

Kuma lallai wannan rana ta cancanci a muhimmantar da ita, domin rana ce wacce a cikinta aka kammala addini kuma aka cika ni’ima wanda Qur’ani ne ya nassanta wannan cewa: “A yau na kammala maku addininku kuma na cika ni’imata a kanku kuma na yarda Musulunci ya zama addini a gare ku”. (Suratul Ma’ida, aya ta 3). Kuma tabbas addini ya kammalu ne, ni’ima ma ta cika ne da nassanta Ali dan Abu Dalib a matsayin kalifan Manzon Allah (s.a.w.a) kuma shugaban muminai, sannan a bayansa kuma ‘ya’yansa Ma’asumai (as) su ne shuwagabanni, don haka ba wani bakon abu ba ne idan aka ce wannan ranar ita ce mafi girman Idodi a Musulunci, kuma ya zo a cikin ruwayar da ta gabata daga Imam Ridha (as) ya ce: “Lallai ranar Ghadir ta fi shahara sama a kan kasa”.

Manzon Allah (s.a.w.a) da alayensa (as) suna yin farin ciki saboda halartar taron miliyoyi a makwancin Amirul muminina (as) a ranar Ghadir, domin hakan yana jawo hankalin al’ummar duniya, don kuwa ita wannan ranar ita ce ta nuna inda ya kamata mutane su dosa a rayuwarsu a gaba, kuma ita ce ta iyakance wa al’umma hanyar da za su bi a cikin wannan rana mai cike da tarihi, ta yadda al’umma ba za ta kidime ta juya baya bayan wafatin Annabinta (s.a.w.a) ba, duk da cewa an samu wasu daga cikin wadanda suka gabata sun aikata hakan.

Lallai halartar miliyoyi masu ziyarar Arbaeen sun janyo hankula game da al’amarin Imam Husain (as), har ta kai ga da yawa daga cikin mutane ma’abota addinai daban-daban da mazhabobi daban-daban suna yin bincike game da wannan hakikar mai cike da ban al’ajabi kuma suna sanin abin da ya wakana ta yadda har yakan kai su ga sun zubar da kwalla da yin bakin cikin kisan gillar da aka yi wa jikan Manzon Allah (s.a.w.a), suna masu bijirewa wanda ya aikata wannan danyan aiki wato Yazid, sai dai har yanzu al’umma ba ta gama fahimtar kammalallun natijoji masu albarka na wannan waki’ar (ta karbala ba).

To da za a samu irin wannan halarta ta miliyoyi a ranar Ghadir – ko da bayan wasu shekaru ne – har sakamakon hakan ya janyo hankula zuwa ga lamarin to lallai hakan taimakawa ce ga Manzon Allah (s.a.w.a), kuma raddi ne ga wanda ya riya cewa ai ya yi wafati ba tare da ya kalifantar da kowa a bayansa ba, wanda hakan ya sabawa hikima a sirar masu hankali, haka nan za mu fahimtar da al’ummar duniya hakikanin abin da ya gudana.

Lallai a samun miliyoyi suna raya irin wannan munasaba kyautatawa ce ga Amiril muminina (as), sannan rage girman zaluncin da aka yi masa ne kuma shaidawa ce ga hakkinsa da aka danne masa, bugu-da-kari shelantawa ce ga raya al’amarin Ahlul Bait (as), kuma shimfida ce ga bayyanar Imam Mahdi (aj) wanda yake tarbar masoya masu ziyara (yana masu maraba lale da zuwa) wadanda suke yi masu fatan dukkan alheri da dacewa.

A saboda haka ka da ku tozarta wannan damar mai girman daraja, ku yi kokari sunayenku su shiga cikin wadanda suke taimakon Allah Ta’ala da Manzonsa (s.a.w.a) da Amirul muminina (as), kuma ku faranta masu rayukansu (tsirar Allah da amincinsa ya tabbata a gare su).

Kuma muna kira ga wadanda Allah ya hore masu da masu maukibobi su yalwata abinci da sauran kayan bukatu ga baki masu girma masu ziyara.

Mas’ala: Ta yiwu wani muminin ya ce ba zai sami zuwa ba saboda yana son ya azumci wannan yinin saboda tarin ladar da ke cikin yinsa, ga shi kuma tafiya ba za ta bar shi ya iya yin azumin ba. To a nan sai mu ce: Ai ladar ziyara ta fi tarin yawa, sannan mai ziyara zai ma iya kame bakinsa a yayin tafiyar sai daga baya ya kuduri niyyar yin azumin bayan ya koma gida ko da ko saura ‘yan mintuna ne rana ta fadi, saboda shi azumin nafila ba a shardanta sai mutum ya zamanto yana gida yayin zawali ba, don haka shi za a iya yin niyya ko da rana ta kusan faduwa ne.

 

Muhammadul Yaqubi – Najaf mai Tsarki.

16 – Zulhijja – 1440H.

18 – 08 – 2019M.